Rikiji Ya Nuna Sha'awarsa Ga Jamiyyar APC Don Tsayawa Takarar Sanata A Zamfara

Rikiji Ya Nuna Sha'awarsa Ga Jamiyyar APC Don Tsayawa Takarar Sanata A Zamfara

Daga Hussaini Ibrahim
Hausawa na cewa, ba'a fafe gora ranar tafiya,tunkafin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta ayyana zaben cika gurbi na Dan Majalisar Datawa mi wakiltat Zamfara ta tsakiya,  Tsahon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara,Hon Sunusi Rikiji ya garzaya Hedikwatar Jamiyyar APC ta Jihar Zamfara,dan mika kokon barar sa ga Uwar Jamiyyar na tsayawa takara  Sanata mai wakiltat Zamfara ta tsakiya a Majalisar Datawa ta qasa, sakamakon , Hassan Nasiha da ya aje kujerar Sanata gwamna Matawale ya bashi Mataimakin sa a watan da ya gabata.
Sunusi Rikiji ya garzaya Hedikwatar Jamiyyar APC na Jihar Zamfara,dan ya tabbatar masu da cewa,yana da shiawar tsayawa takara Sanata mai wakiltat Zamfara ta tsakiya a Majalisar Datawa.domin Cika Gurbi sa a Majalisar.
Rikiji wanda  ya kwashe shukaru Takwas yana Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Zamfara,zango biyu . Kuma yanzu haka shine shugaban Ma'ainatan Kakakin Majalisar Tarayya , Karkashin Jagoranci Hon Femi Gbajablamula.
Kuma ya tabbatar wa Jamiyyar APC cewa,idan suka tsada shi a matsayin Dan takara Sanata ,insha Allah zai kawo ma yankinsa cigaba,wajan tattalin arziki da tsaro da jindadin al'umma da walwalarsu.
Anasa jawabin Shugaban Jamiyyar APC na Jihar Zamfara,Alhaji Tukur Dan Fulani yanuna matukar farin cikin sa kan wannan bukatar ta Hon Rikiji.kuma ya tabbatar da cewa, Rikiji yayi abunda ya kamata Kuma alokacin da ya kamata na mutunta Jamiyyar da 'yan Jamiyyar  kuma da yardar Allah zamuyi abunda ya dace akan wannan bukata ta Hon Rikiji.
Akan haka ne Shugaban Jamiyyar APC Alhaji Tukur Dan Fulani yayi kira ga 'yan Jamiyyar su da suyi koyi da Hon Rikiji wajan mutunta Shugabannin Jamiyyar da 'yan Jamiyyar wajn neman takara a kowace kujera ta mukamin siyasa.