Sanata Lamido Ya Yi Ta'aziyar Rasuwar Jelani Ɗanbuga  

Sanata Lamido Ya Yi Ta'aziyar Rasuwar Jelani Ɗanbuga  

 

Sanata Ibrahim Lamido ya yi ta'aziyar rasuwar dan Majalisar Tarayyar mai wakiltar Isa da Sabon Birni daga jihar Sokoto a Najeriya , Abdulkadir Jelani Danbuga.

Sanata Ibrahim Lamido a sanarwar ta'aziya da ya fitar jim kadan bayan kammala janazar margayin ya bayyana rashi ne aka yi ba a Sabon Birni kadai ba, a Sokoto baki daya.

Sanata Lamido wanda yake a kasa Mai tsarki ya nuna kaduwarsa da rashin mutum nagari Mai kirki bayan gajeruwar rashin lafiya.

Sanata ya mika sakon ta'aziyarsa ga Gwamnan Sokoto Dakta Ahmad Aliyu da Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko da iyalan margayin da mutanen Sokoto baki daya.

Ya roki Allah ya gafartawa Ɗanbuga ya Kuma isar masa ga abin da ya bari.