Daga Hussaini Ibrahim.
Gamayyar kungiyar Daliban Arewa ta tabayyana cewa ayyukan ‘yan ta'adda na faruwa ne sakamakon rashin kishin kasa, da rashin gaskiya da talauci da ya addabi al’umma,kuma yayi sanadiyar tarwatsa cigaban area, sakamakon haka ne suka yi kira ga Gwamnatin Tarayya da a kafa hukumar raya yankin Arewa maso yamma.
Kungiyar tayi wannan kiran ne a jiya Talatar da ta gabata a taron kungiyar hadin kan dalibai ta Arewa ta shirya a kwalejin kimiya da fasaha ta tarayya da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara.
Shugaban gamayyar kungiyoyin masu zaman kansu na jihar Zamfara Ambasada Ibrahim Tudu ya ce kafa hukumar raya yankin arewa maso yamma zai magance kalubale da dama. na rashin tsaro a yankin.
A nasa jawabin Dr Abdulrahman na jami’ar tarayya ta Gusau, ya ce talauci ya yi yawa arewa katutu da ranshin zuwa makaranta ga matasa ,wannan ya sanya matasan ke shiga kungiyoyin bata gari.sai dai in Shabani sun canza halayan su na tunanin gina al'umma da cigaban ta.inji Dr Abdurahman.
Dr ya ci gaba da cewa jawabinsa ya ginasa ne akan akan wani bangare ne na jerin laccar marigayi Maitama Sule Dan Masanin Kano, mai taken rashin tsaro: yin tambayoyi kan illar ‘yan fashi da makami da ilimi da ci gaban Arewacin Najeriya.
"Idan ba mu canza tunani da dabi'unmuba da halayenmu ba na samun arziki ta kowane hali za mu ci gaba da kasancewa cikin matsalolin rashin tsaro da ta'addanci".
A nasa Shugaban Taron ,shugaban kungiyar hadin kan kungiyoyi masu zaman kansu ta jihar Zamfara (NGOS) Mallam Ibrahim Tudu ya ce arewa na bukatar hukumar cigaban ta kamar sauran yankunan kasar nan.
"Muna bukatar hukumar raya arewa maso yamma, kamar hukumar raya yankin Neja-Delta domin samun albarkatunmu da tsare-tsaren ci gaban yankinmu".
Tun da farko, babban kodinetan kungiyoyin Arewa na kasa, Jamilu Ibrahim charanchi ya ce burinsu shi ne su hada kan matasa a matsayin masu rike da madafun iko dan samun ingantaciyar rayuwa ga al'umma.
"Kuma zai samar da ingantaccen jagoranci, da rikon amana mai dorewar bisa tausan al'umma da cigaban su".
Wani bangare na aikinsu Kungiyar shi ne na ba da shawarwari domin samar da sabbin shugabannin amintatu wadanda suka san matsalar al'umma da yadda zasu gyarata .