Gwamnatin Zamfara ta samar wa manoma da Takin zamani  a kan kudi 7,000 a kowane buhu

Gwamnatin Zamfara ta samar wa manoma da Takin zamani  a kan kudi 7,000 a kowane buhu

Daga Aminu Abdullahi Gusau.
 
Gwamnatin jihar Zamfara ta ce ta samar da takin zamani ga kanana da manyan manoma da ke fadin jihar har Tirela saba'in 70, kuma ta umurci da a sayar masu da duk buhu daya akan kudi naira dubu bakwai N7, 000 domin saukaka masu yin noma a wannan shekara.
 
Kwamishinan kananan hukumomi da cigaban al'umma Alhaji Abubakar Sarkin Pawa Dambo ne ya bayyana hakan a lokacin da yake yiwa manema labarai bayani dangane da wata murya dake yawo a kafafen sada zumunta tana cewa gwamnatin Zamfara tana sayar da Takin zamanin akan kudi naira dubu goma sha biyu, N12,000.

 
Kwamishinan ya kara da cewa, sanin kowa ne gwamna Matawalle ya ba da umurnin saye da raba wa kananan hukumomi goma sha hudu dake fadin jihar Tirela 70, inda ma'aikatar ta kananan hukumomi ta yi taro da sakatarorin dake a kowace karamar hukuma kuma suka ba kowannen su kason karamar hukumar sa.
 
"Mun karbi kason takin na kowace karamar hukuma a ma'aikatar gona ta jihar kuma mun bada shi ga kowane sakataren karamar hukuma, kuma mun umur cesu dasu sayar wa manoma takin akan kudi naira dubu bakwai,  ba dubu goma sha biyu ba.
 
"Amma abun ban mamaki saiga wasu don ra'ayin kansu sun shiga kafar yada labarai ta intranet suna cewa wai gwamnati tana sayarwa manya da kananan manoma takin zamani akan kudi naira dubu goma sha biyu.
 
" Ina yiwa manoman jihar Zamfara albishir cewa wannnan maganar karya ce, gwamnati ta bayar da umurnin sayarwa manoma taki akan kudi naira dubu bakwai kacal domin a tallafa masu."inji Dambo.

 
Daga karshe ya shedawa manoman na Zamfara cewa su yi watsi da wannan magana domin ba a bangaren gwamnati ta fito ba.