Shugaba Buhari Ya Nada Salihu Dembo Matsayin Sabon Shugaban Gidan Talabijin Na Kasa NTA

Shugaba Buhari Ya Nada Salihu Dembo Matsayin Sabon Shugaban Gidan Talabijin Na Kasa NTA

 

By Jabir Ridwan 

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada sabon Darakta janar na gidan talavijin na kasa NTA.

 
Ministan yada labarai da al'adu Lai Muhammad shi ne ya sanarda Hakan a cikin wani bayani da ya fitar a ranar laraba.
 
Bayanin yakara da cewa wannan nadin nada wa'adi na shekara uku.
 
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, Mr salihu Dambos sabon daraktan kafin nadin shi, ya kasance shugaban sashen Kasuwanci na gidan talabijin na kasa waton NTA, Kuma ya shafe tsawon shekaru 20 cikin aikin jarida.
 
Bayanin yakara dacewa Dembos ya taba Rika mukamin janar manaja na tashar a jahohin kogi, Kano tare da zamowa babban Jami'i a tashar NTA Dake Kaduna da dai sauran mukamai.