'Sarakuna ba Su Tsoron Gwamnoni,' Sai dai----Sarkin Musulmi

'Sarakuna ba Su Tsoron Gwamnoni,' Sai dai----Sarkin Musulmi

Mai alfarma sarkin Musulmi, Sa'ad Mohammad Abubakar II, ya karyata masu cewa sarakunan gargajiya na tsoron gwamnonin Najeriya. Sarki Sa'ad Abubakar II ya ce tun kafin a ba Najeriya 'yanci a shekarar 1960 sarakunan gargajiya ke mulki a kasar nan. 
Jaridar Daily Trust ta rahoto sarkin na cewa sarakunan gargajiya sun fi gwamnoni alakar kusa da mutane kuma sun fi su fahimtar halin da kasar ke ciki. 
Ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Talata a taron masu ruwa da tsaki kan ci gaban matasan Arewacin Najeriya, wanda gidauniyar tunawa da Sir Ahmadu Bello ta shirya. Maganar sarkin Musulman martani ce ga kalaman tsohon gwamnan Neja, Babangida Aliyu, wanda ya ce sarakunan gargajiya na tsoron gwamnonin jihohinsu. 
“Na ji cewa sarakunan gargajiya na tsoron gwamnoninsu. Ba haka ba ne, sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoninsu. 
Mai alfarma Sa'ad Abubakar II ya ce duk abin da Allah ya kaddara ne ke faruwa, kuma da aka kawo tsari na dimokuradiyya, sarakunan sun karba hannu biyu biyu. "Saboda dukkaninmu mun sani, kafin a kawo tsarin shugabanci na gwamnoni sarakunan gargajiya ne ke mulkar Najeriya tun 1914." "Sarakunan gargajiya na girmama gwamnoni ne kawai, suna girmama gwamnoni saboda suna da iko a jihohohin da suke mulka, amma ba wai tsoro ba."