Atiku Ya zabi Gwamnan Jihar Delta Ya Zama Mataimakinsa

Atiku Ya zabi Gwamnan Jihar Delta Ya Zama Mataimakinsa


Atiku Abubakar, dan takarar shugabancin kasar Nijeriya karkashin jam'iyyar PDP, ya zabi Ifeanyi Okowa, gwamnan jihar Delta a matsayin abokin tafiyarsa a zaben 2023. 
Kwamitin gudanar da ayyuka na jam'iyyar PDP a ranar Laraba sun zabi Nyesom Wike, gwamnan jihar Ribas, a matsayin wanda zai kasance mataimakin dan takarar shugabancin kasar. 
 Mambobin majalisar gudanarwar jam'iyar  sun yi zabe inda Wike ya samu kuri'u 13 yayin da Okowa ya samu uku kacal, lamarin da yasa masu ruwa da tsakin suka aminta da Wike.
Sai dai, Atiku Abubkar an  gano ya kasa sakin jiki da Wike a matsayin abokin tafiyarsa saboda ya sakankance cewa gwamnan baya kaunarsa a gidan siyasa yi masa mataimaki zai yi wuya. 
Wasu manya a PDP an gano ba su aminta da Wike ba saboda tsananin kusancin mataimakin shugaban kasa da kujerar shugabancin kasar. 
Atiku ya sanar da zaben mataimakinsa da kansa a babban zauren PDP abin da aka nuna gamsuwa bayan ya sanar da zabin da ya yi kan Okowa.