Amaechi ya faɗi dalilinsa na daina magana kan siyasar Nijeriya 

Amaechi ya faɗi dalilinsa na daina magana kan siyasar Nijeriya 

Tsohon Ministan Sufuri a Najeriya Rotimi Amaechi ya ce an daina jin ɗuriyarsa ne a fagen siyasar Najeriya saboda "babu wani sabon abu" da zai faɗa.

Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya riƙe muƙamin minista a gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari daga 2015 zuwa 2022, bayan ya mulki jihar tasa a kudancin Najeriya tsawon shekara takwas.

"Babu wani sabon abu kwatakwata," in ji ɗan siyasar wanda ya nemi takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar APC mai mulki cikin hira ta musamman da BBC.

"Abubuwan da ake so na yi magana a kan su suna nan kuma tun shekarun 1970 aka fara magana a kansu. Talauci, yunwa, rashin ingataccen ilimi, fashi, sata, cinhanci da rashawa, duka suna nan. Akwai abin da ya sauya ne?"

Haka nan, Amaechi ya riƙe muƙamin kakakin majalisar dokoki ta jihar Rivers mai arzikin man fetur daga 1999 zuwa 2007.

Yana cikin gwamnonin da suka kafa sansanin tawaye a jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya a lokacin da yake gwamna, inda suka yaƙi Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan, abin da ya kai ga faɗuwar gwamnatin a zaɓen shugaban ƙasa na 2015.