Fin Karfi: Mata Ta Sumar Da Mijinta Bayan Ta Lakada Masa Duka

Wata mata ta sumar da mijinta bayan ta lakada masa duka a layin Lambe Iluyomade a Ago Okota da ke cikin jihar Lagos. Mutumin mai suna Edwin Ugwu dan shekara 56 ya labartawa kotun majistare a jihar Lagos yadda matarsa mai suna Ebere ta ke dukansa da zaran ya mata wani laifin da bai kai komai ba.
Miji ya ce irin azabtar da shi ta take yi da yawa wanda har ya kai ga lakada masa dukan da ya suma aka wuce dashi asibiti, jaridar Daily Trust ta tattaro.
Dan sanda mai gabatar da kara, DSP Kehinde Ajayi, ya ce ma’auratan suna zaune ne a layin Lambe Iluyomade a Ago Okota dake cikin jihar Lagos, sun samu sabani wadda har ya kai ga tashin jijiyoyin wuya kafin matar Edwin ta daka shi wadda ya yi sanadiyyar suma tare da kai shi asibiti don ceto rayuwarsa.
Har ila yau rahotanni sun tabbatar da cewa matar da ake zargi ta musanta laifukan da ake tuhumarta da shi na cin zarafi da wulakanta dan Adam.
Daga bisani, dan sanda mai gabatar da kara ya nemi kotun da ta bada ranar da za a ci gaba da zaman sauraren wannan karar. Mai shari’a, Mrs E. Kubeniji ta bada belin wacce ake karan akan kudi N100,000 da shaidu guda 2, sannan ta daga sauraren karar zuwa 6 ga watan Yuni na wannan shekara.