Jagororin Jam'iyyar PDP a Jihohin Arewa 19 sun amince da zaɓen tsohon shugaban majalisar dattawa ta Ƙasa, tsohon ministan Ilmin Najeriya, tsohon ministan Muhalli, tsohon ministan Masana'antu, tsohon ministan harkokin cikin gida, tsohon malamin Jami'a, tsohon shugaban Ƙungiyar ASUU reshen Jami'ar Jos, Sanata Dakta Iyorchia Ayu daga ƙaramar hukumar Gboko ta Jihar Binuwai domin ya yi takarar shugabancin Jam'iyyar PDP na Ƙasa shi kaɗai ba hamayya.
Shugaban kwamitin shirya babban taro na ƙasa Gwamnan Adamawa Ahmadu Ummaru Fintiri ne ya sanar da matsayar ta jagororin PDP a Arewa domin kara hada kai a tafiyar a samu nasara a 2023.
Shi ma ɗan takarar da aka tsayar ya godewa jagororin da alƙawanta aiki tuƙuru don samar da nasarar PDP.