Tsohon mataimakin gwamnan Sakkwato kana mininstan albarkatun ruwa a Nijeriya Mukhtari Shehu Shagari daya daga cikin manyan 'yan takarar gwamna a jam'iyar PDP ya aiyana zai tsaya takarar gwamnan jihar Sakkwato tare da gabatar da Fom da ya saya a idikwatar jam'iya a Abuja domin shugabannin jam'iya da al'ummar Sakkwato su sani ba wasa a cikin tafiyarsa.
Barista Mukhtari Shagari a wannan alhamis tare da dimbin magoya bayansa suka hallara a hidikwatar jam'iya matakin jiha in da ya bayyana ba wanda ya kai shi cancanta in adalci za a yi shi yafi cancantar a bar masa, amma dai duk wanda ya fito zai yi neman kujerar a tare da shi ya sani shi ya shirya.
Barista ya yi shagube kan cancantar sama da saura ya ce "Na yarda na tsaya in da nake ba tare da sauya jam'iyya ba tun da aka kafa PDP ina cikinta, ina son jam'iyyar PDP domin tsarinta, na kuma yarda da duk abin da jam'iyar ta yanke bana gardama zan bi shi a koyaushe.
"Allah ne ya kaddari na zama kwamishina na kuma zama minista da mataimakin gwammna ba tare da roki kowane mutum ba, ina kan wannan tsarin nasan Allah ne yake bayar da mulki a duk sanda ya so kan haka nake kira ga mutanen Sakkwato da suka yarda da siyasar cigaba su zo mu hada kai domin al'umma ta gari," a cewarsa.
Ya kara da cewar ya fito takarar ne a yanzu bayan zamansa kwamishinan shari'a a jihar Sakkwato ya yi ministan Ruwa a tarayyar Nijeriya ya kuma zama mataimkin gwamnan Sakkwato shekara takwas, "a halin da muke ciki karkashin wannan gwamnati ta mai girma Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal an samu cigaba wajen tarbiyar yara da aiyukka da sha'anin lafiya da tsaro da ilmi da sauran abubuwan rayuwa, kan haka naga ba daidai ba ne na zauna da irin fasaha da kwarewa da Allah ya bani bayan karewar gwamnatin nan abubuwa a jiha su koma baya dole ne a samu mutum wanda ba dan dagaji ba ne, yana da kwarewa da iya kula da dukiyar jama'a ba tare da an sace ta ba, ya yi wa jama'a aiki yanda yakamata, ya kuma rungumi talakawa don magance matsalolin da suka dame su.
"A wannan lokaci in nace ba zan fito takara ba, na cuta ma mutanen Sakkwato, kuma ni buri na shi ne jihar Sakkwato tafi kowace jiha a Nijeriya, da ikon Allah in na zama Gwamnan Sakkwato za ta zama kan gaba ga duk abin da za a yi," kalaman Barista Shagari.
Ya kara da cewar zai cigaba da daukaka jihar Sakkwato mutane sun sani a lokacin da yake minista ba wani minista da ake magana sama da shi, zai tabbatar da talakan Sakkwato ya san akwai gwamnati akan aiyukkan da Tambuwal yake yi zai daura.