Gwamna Bago Ya Rushe Majalisar Zartarwa a Neja

Gwamna Bago Ya Rushe Majalisar Zartarwa a Neja

Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya rusa majalisar zartarwar jiharsa tare da sallamar dukkan kwamishinoni.

Salinga TV ta ruwaito cewa sanarwar rushewar ta fito ne daga mai magana da yawun gwamnan, Bologi Ibrahim, a ranar Litinin, 1 ga Satumba, 2025.

Sanarwar ta ce gwamnan ya bayyana hakan yayin taron majalisar zartarwa da aka gudanar a Minna, inda ya gode wa mambobin majalisar bisa gudummawar da suka bayar tare da yi musu fatan nasara a ayyukansu na gaba.

Sai dai sanarwar ta bayyana cewa Sakataren Gwamnati na Jihar, Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin, mataimakin gwamna da wasu manyan jami’an ofishin gwamna za su ci gaba da rike mukamansu.