Shugaban Kula Da Allurar Rigakafin Foliyo A Kebbi Ya Shawarci Iyaye Kan Rigakafin 

Shugaban ya kuma kara jawo hankalin magidanta su rika sanya iyalansu suna tsaftace muhallan su kamar cikin dakunan su da filayen gidajen su da kofar gidajen su da kuma jikinsu, ya kuma ce su rika barin matan su masu juna biyu suna zuwa asibiti domin awon ciki, kuma su kai yaran su asibiti acika yi masu dukkan alluran da suka dace bayan haihuwar su. Shugaban ya kuma yi kira ga shugabannin al’umma sarakuna su cigaba da taimakawa wajen kara wayewa al’ummar su kai muhimmancin wannan allurar rigakafin da kuma tura mata masu ciki zuwa asibiti tare da kananan yara, kuma ya shawarci iyaye maza da mata su bayar da  hadin kai kwalliya ta biya kudin sabulu duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Shugaban Kula Da Allurar Rigakafin Foliyo A Kebbi Ya Shawarci Iyaye Kan Rigakafin 
Gov. Bagudu

SHUGABAN KULA DA ALLURAN RIGAKAFIN FOLIYO NA ASUSUN MAJALISAR DUNKIN DINIYA UNICEF NA JIHAR KEBBI YA SHAWARCI IYAYE.

 

Daga Bashir LawalZakka, Birnin Kebbi.

Shugaban kula da alluran rigakafin foliyo na asusun majalisar dinkin duniya (unisef) a Jihar Kebbi Mr. Nathaniel Rock, ya shawarci magidanta su  daure wajan bayar da ya’yansu don a gida masu alurar rigakafin foliyo a duk lokacin da jami’an aikin rigakafin suka je gidajensu.

Shugaban shirin ya bada wannan shawarar ce a wani taron yan’jaridada ya kira wanda akayi a dakin taro na sakatariya Gwamnatin Jihar Kebbi, akan muhimmancin alluran rigakafin foliyo Mr. Nathaniel Rock yace babu wata mastala da ke tattare da allurer rigakafin shan inna, kuma rashin yin allurar rigakafin babbar barazana ce ga lafiyar yara, yace masu adawa da allurar su sani cewa bada Nijeriya kawai suke yi ba, likitotin duniya ne baki daya.

Shugaban ya kuma kara jawo hankalin magidanta su rika sanya iyalansu suna tsaftace muhallan su kamar cikin dakunan su da filayen gidajen su da kofar gidajen su da kuma jikinsu, ya kuma ce su rika barin matan su masu juna biyu suna zuwa asibiti domin awon ciki, kuma su kai yaran su asibiti acika yi masu dukkan alluran da suka dace bayan haihuwar su.

Shugaban ya kuma yi kira ga shugabannin al’umma sarakuna su cigaba da taimakawa wajen kara wayewa al’ummar su kai muhimmancin wannan allurar rigakafin da kuma tura mata masu ciki zuwa asibiti tare da kananan yara, kuma ya shawarci iyaye maza da mata su bayar da  hadin kai kwalliya ta biya kudin sabulu duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

A karshe ya shawarci shugannin addinai su jahankalin maza da mata a wuraren ibada don samun nasarar shirin, yace an dade ana yin wannan allurer rigafin kuma babu wata matsala tattare dashi, da akwai illa ba zasu bari akawo wa mutanen su ba, kuma shugannin arewa basu yarda da shirin ba.