Yadda 'Yan Bindiga da Dama Suka Halaka Yayin Harin Soja a Sokoto

Yadda 'Yan Bindiga da Dama Suka Halaka Yayin Harin Soja a Sokoto

Rayukan ƴan bindiga da dama sun salwanta yayin da suka kai harin ramuwar gayya a ƙauyen Tukandu da ke ƙarkashin gundumar Sakkwai a ƙaramar hukumar Tangaza ta jihar Sokoto. Daily Trust ta ce ƴan bindigan sun gamu da ajalinsu ne lokacin da suka shiga ƙauyen da misalin ƙarfe 2:00 na rana a ranar Talata, 24 ga watan Oktoba, domin ɗaukar fansa kan kisan da aka yi wa wani ɗan bindiga a ranar Litinin. 
An bayyana cewa ƴan bindigan sun yi yunkurin kai hari ƙauyen ne a ranar Litinin amma sun fuskanci turjiya daga mutanen ƙauyen, lamarin da ya yi sanadiyyar kashe mutum biyu ciki har da wani ɗan bindiga. 
Tsammanin cewa ƴan bindigan za su kawo harin ramuwar gayya ya sanya mazauna ƙauyen suka tsere inda suka bar jami'an soji da aka tura domin dawo da zaman lafiya a ƙauyen. LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng Ƴan bindigan da ba su san da wannan shirin ba, sun kai farmaki ƙauyen ne da misalin ƙarfe 10:00 na safe, amma sai sojoji suka yi artabu da su wanda ya ɗauki tsawon lokaci. Wani mazaunin yankin da ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce an kashe ƴan bindiga da dama a yayin da wani jami'in soji ɗaya ya samu raunuka. 
Ya ƙara da cewa an ƙwato babura guda 12 da bindigogi ƙirar AK 47 guda uku daga hannun ƴan bindigan. Mai baiwa Gwamna Ahmed Aliyu shawara kan harkokin tsaro, Kanal Ahmed Usman (mai ritaya) ya tabbatar da aukuwar lamarin.