Abin Da Ya Sa ‘Yan Bindiga Suka Sace Shugaban Karamar Hukuma a Nasarawa

Abin Da Ya Sa ‘Yan Bindiga Suka Sace Shugaban Karamar Hukuma a Nasarawa

Wasu 'yan bindiga waɗanda aka yi imani cewa maharani daji ne sun sace shugaban ƙaramar hukumar Akwanga, Safiyanu Isa-Andaha a jihar Nasarawa da ke tsakiyar Najeriya.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandar jihar, DSP Ramhan Nansel ya tabbatarwa da BBC cewa suna bincike kan batun sace shugaban ƙaramar hukumar.

Rundunar ta kuma ce ta baza jami'ai domin ceto shugaban ƙaramar hukumar da kuma sauran mutanen da aka sace.

Bayanai sun nuna cewa 'yan fashin sun yi awon gaba da shugaban ƙaramar hukumar ne da sauran wasu mutane a ƙauyen Ningo cikin daren Talata.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya kuma ambato Haruna Kassimu, mataimaki na musamman ga gwamnan jihar kan harkokin ƙananan hukumomi da masarautu kuma amini ga shugaban ƙaramar hukumar yana tabbatar da rahoton.

Matsalar satar mutane domin karɓar kuɗin fansa, na ci gaba da ƙamari a jihar ta Nasarawa, wadda ta fuskanci irin hakan a kan wasu manyan jami'an gwamnati da daidaikun mutane da kuma ɗaliban jami'a a jihar.

Kasar ta kwashe tsawon shekaru tana fama da matsalar tsaro daga ƙungiyoyin masu dauke da makamai irinsu Boko Haram da ISWAP, yayin da matsalar 'yan fashin daji masu satar mutane domin karɓar kuɗin fansa ke ta'azzara hakan ya sa ake zaton an sace shugaban ne domin karbar kudin fansa.