Miyagu Sun Matsa da Sace Sarakuna, An Ɗauke Hakimi da Ɗiyarsa a Kaduna 

Miyagu Sun Matsa da Sace Sarakuna, An Ɗauke Hakimi da Ɗiyarsa a Kaduna 

 
Masu garkuwa da mutane sun kai hari kan mazauna yankin Gurzan Kurama a daren Asabar inda su ka ɗauke mutane da dama. 
Kungiyar mazauna Kaduna ta Kudu (SOKAPU) da ta tabbatar da harin, ta bayyana cewa ƴan ta'addan sun sace karin mutane shida. 
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa miyagun sun sace hakimin yankin, Yakubu Jadi da ɗiyarsa, sai Iliya Yakubu, Nehemiah Tanko da Thomas Tanko. 
Lamarin sace masu rike da sarautun gargajiya na kara kamari a yankin Arewa maso Yammacin kasar nan, Channels Television ta wallafa.
Jami'in kungiyar mazauna Kaduna ta Kudu (SOKAPU), Josiah Yusuf Abraks ya nemi daukin jami'an tsaron kasar nan wajen ceto hakimin Gurzan Kurama. 
Josiah ya kara da cewa iyalai da yan uwan wadanda aka sace sun fada mawuyacin hali, kuma akwai bukatar cetonsu cikin gaggawa. 
Kungiyar SOKAPU ta ce akwai bukatar jama'a su rika ɗari-ɗari da baƙin fuska da ke gewaye a yankinsu. Kakakin SOKAPU, Josiah Yusuf Abraks ya shawarci mazauna yankin su rika sa ido sosai akan bakin fuska da ke shige da fice a yankin, domin daƙile ayyukan sace jama'a.