Dalilin da ya sa Likitocin Nijeriya suka shiga yajin aiki

Dalilin da ya sa Likitocin Nijeriya suka shiga yajin aiki

Ƙungiyar Likitoci masu neman ƙwarewa ta Najeriya (NARD) ta fara yajin aikin gargadi na kwana bakwai a dukkanin cibiyoyinta na faɗin ƙasar, inda ta buƙaci a sako Dakta Ganiyat Popoola, mambarsa da ke hannun masu garkuwa da mutane tsawon wata takwas.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito cewa shugaban NARD, Dakta Dele Abdullahi ne ya sanar da fara yajin aikin a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya bayyana cewa za a fara yajin aikin da ƙarfe 12:00 na safe a ranar Litinin 26 ga watan Agusta, 2024.

An yanke shawarar yajin aikin ne a wani taron gaggawa da jagororin ƙungiyar suka gudanar a ranar Lahadi, 25 ga Agusta, 2024.

An sace Dokta Ganiyat Popoola, magatakarda a sashin kula da ido da ke Babban Asitin Ido na ƙasa da ke Kaduna ne, kusan wata 8 da suka gabata, tare da mijinta da kuma ɗan uwanta.

Sai dai an saki mijinta a watan Maris, amma aka ci gaba da riƙe Popoola da dan uwanta.

Makonni da suka gabata, mambobin NARD sun yi zanga-zanga a dukkan manyan asibitocin ƙasar, don neman a gaggauta sakinta.