Boko Haram: 'Yan Matan Chibok 98 Suka Rage a Hannun 'Yan Ta'adda---Hukumar Soji

Boko Haram: 'Yan Matan Chibok 98 Suka Rage a Hannun 'Yan Ta'adda---Hukumar Soji

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa har yanzu akwai sauran yan matan makarantar Chibok guda 98 tsare a hannun yan ta’addan Boko Haram. A ranar 14 ga watan Afrilu ne yan ta'addan suka farmaki makarantar firamare ta yan mata da ke Chibok a jihar Borno inda suka sace dalibai 276.
Shugaban sashin bayanan sirri na rundunar Operation Hadinkai da ke yaki da ta’addanci a Arewa maso gabas, Kanal Obinna Ezuipke, ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga manema labarai a hedkwatar rundunar da ke Maimalari a Maiduguri. 
“Daga cikin yan matan Chibok 276 da aka sace, yan mata 57 sun tsere a 2014 yayin da aka saki yan mata 107 a 2018. An ceto yan mata uku a 2019, biyu a 2021 sannan an ceto 9 a 2022, wanda jimilarsu ya zama 178 sun kubuta yayin da 98 suka yi saura a hannun Boko Haram.” Da yake bayar da jawabi kan ayyukan dakarun Operation Hadinkai a Agustan 2022, Kanal Ezuipke ya bayyana cewa an kashe jimilar yan ta’adda 43, yayin da sojojin suka kama wasu 24 a watan Agusta kadai, baya ga sama da 100 da aka kashe a watan Satumban 2022. 
Har ila yau, ya ce an kwato makamai da suka hada da bindigogin AK-47 129, alburusai 1,515, bindigogi 16 da sauransu.
Ezuipke ya bayyana cewa sojojin sun samu hare-hare 26 daga yan ta’addan, kuma a cikin haka, an kashe sojoji biyu kuma wasu 9 sun jikkata. Ya kara da cewa sojojin sun aiwatar da fatrol 2726 da kautan bauna 982 kan yan ta’addan. Da yake martani kan kamun masu kaiwa Boko Haram kaya, Ezuipke ya bayyana cewa daga watan Yuni 2022 zuwa yanzu, an kama mutum 113 da ke kaiwa yan ta’addan abinci, taki da sauran kayan amfani.