Mawaƙa Mata Na Ƙadiriyya Sun Gudanar Da Taron Addu'a Da Faɗakarwa A Kano

Mawaƙa Mata Na Ƙadiriyya Sun Gudanar Da Taron Addu'a Da Faɗakarwa A Kano

Daga Ibrahim Hamisu, Kano.

Ƙungiyar Shu'ara'ul ƙadiriyya wato ƙungiyar Mawaƙa Mata na ƙadiryya ta ƙasa ta gabatar da taron addu'oi  da kuma fadakarwa ga mata, da ya gudana a gudana a gidan Sayyidi Yahaya da ke unguwar Gwamnansa, Kano a ranar Asabar da ta gabata,

Babbar baƙuwa a wajen taron, Kwamishiniyar harkokin mata ta jihar Kano, Dr. Zahra'u Muhammad ta bayyana jin daɗin ta da ta halacci wannan taro, sannan ta tabbatar da kudirinta gwamnatin Kano na goyon bayan irin wadannan taro na  adduoi da fadakarwa, 

Dakta Zahra'u ta kara da cewa "Mata suna da bukatu da matsaloli da yawa da ke damunsu a cikin ransu, don haka yana da kyau mu riƙa zuwa muna bijiro da bukatunmu, kuma  Allah yana amsawa"

Sannan ta yi kira ga gidajen manyan malamai irin wannan da su rinka shirya taro irin wannan domin muhimmancisa a cikin al'umma.

Mai masaukin baki kuma wacce ta shirya taron Sayyida Umamatu Malam Kabara wacce ita ce shugabar matan ƙungiyar Shu'aratul Qadiriyya ya ƙasa, ganin irin yadda lamurran suke birkicewa kuma suke ƙara dagulewa, musamman a wannan yanki na mu, wannan ne yasa muka ga ya dace mu shirya wannan taro na addu'a domin mu roƙi Ubangiji mu Allah ko ya yaye mana wannan hali da muke ciki,

" domin idan kana sauraron da kallon kafafen ƴada labarai a kasar nan to kullum da abinda za ka ji, wannan ne yasa na yi tunani na ga ya dace mu shirya shirya wannan taro na addu'a ga mata zalla,

"Sannan mu fadakar ga mata, mu kuma sada zumunci".

Ita ma a jawabinta Sayyida Saratu Sheikh Nasiru Kabara ta ce sun shirya taron ne saboda irin halin da ƙasa ta ke ciki na rashin tsaro da matsalolin da na rayuwa ya sa muka shirya taron,

"Kowa yana bukatar addu'a kuma mun sakankance cewa Allah  S.W.T zai amsa mana domin shi ne yace ku rokeni zan amsa maku". A cewar Sayyida Saratu

Taron dai ya samu halartar Malama Fatima Fagge da jami'ar hulda da jama'a ta ma'aikatar Harkokin mata ta jihar Kano Malama Bahijja da dimbin mata da suka zo daga gurare daban-daban.