MEE'AD LABARIN SOYAYYA MAI RIKITARWA:FITA TA SHA BAKWAI

MEE'AD LABARIN SOYAYYA MAI RIKITARWA:FITA TA SHA BAKWAI
          _*MEE'AD*_
37 ~ 38
Safiyar lahadi! baki d'aya illahirin mutanen gidan zaune suke a falo cikinsu harda Hajiya Hindu da jikanunta twins, ba 'abinda suke sai fira da tsokanan juna musanman Majeed da Mee'ad yayinda Amal take can gefe d'aya zaune kusa da Hajiyarta sai ya tsine fuska suke.
Hajiya Hindu da twins suna zaune kusa da Majeed ita kuma Mee'ad tana kusa da Mommyn ta.
Bayan wadansu lokuta Daddy da Abba suka fito suna fira zama sukai kusa da Hajiyarsu suna tsokanar ta. daria suke sosai sai da suka sha hira kafin Daddy ya gyara zama yace Hajiya nasan kinsan abinda ya taramu anan dan haka muna neman addu'arki.
Murmushi Hajiya Hindu tayi kafin tace idan baku manta ba tin lokacin da Allah yayima Alhaji rasuwa na baku umurnin hade kai tare da shawara da junanku kuma naji dadin wannan hadin kan naku Allah yayi muku albarka.Ameeen sukace baki d'ayan su.
Daddy ya gyara zama sannan ya dubi Majeed dake gefen Abba kafin yace Abdulmajeed kai yarone na gari mai cikakken ilimi da tarbiyya. kuma kai dane a gare mu meyi mana biyayya wannan halayyar taka ce ta janyo hankulan mu har mukaga ya dace mu hadaka 'aure da babbar d'iya 'a garemu wato Amal. mun baka aurenta munsa rana nan da 3month bayan kaje gida kafin ka wuce America sai a daura 'auren ku wuce tare.
Murmushin jin dadi Majeed yayi kafin ya furta kalmar Alhamdulillahi a cikin zuciyarsa. dukar dakai kasa yayi kafin yace Daddy na gode sosai kuma na karbi hadin da kuka yimin ina rokon Allah ya sanya 'alkairi ya kuma za'ba abinda yafi alkairi naji dadin hakan sosai Allah ya kara rufa 'asiri.
"Baki dayansu suka 'amsa da Ameeen.
Abba ya ce Allah yayi maka 'albarka ya kuma sanya 'alkairi da 'albarka cikin wannan hadin.
"Ameeen Majeed ya ce.
Gyaran murya Hajiya Hindu tayi kafin tace to kunji ta bakin Ango amma banga kunbi takan Amaryar ba.
Daria sukayi kafin Daddy ya ce aitin a jiya mun gama da fannin Amarya kam yanzu lokaci kawai muke jira.
Mee'ad dake gefen Mommynta sai a lokacin ta mike ta nufi wajen da Amal take zaune kama hannunta tayi fiskarta cike da murmushi tace na tayaki murna yar uwata Allah ya sanya 'alkairi. tana gama fadin haka ta nufi sama zuciyarta cike da damuwa. Majeed yabi bayanta da kallo zuciyarsa cike da sake ~ sake.
Fira sukaci gaba dayi sai daria suke. a lokacin Abba yake shaida ma mutanen gidan tafiyar twins  school a germany. dukkan su sunyi musu fatan alkairi amma banda Umma. 
%%%%%%
Kai tsaye bedroom dinta ta nufa zuciyarta cike da kunci laptop dinta ta dauko ta bude dukkan messages din da suke turama juna, hawaye ne ya gangaro kan kuncinta karanta messages din take cike da damuwa da kuma dana sanin kulla soyayyar boye da tayi tsakaninta da Majeed din.
Jingina kanta tayi bisa gado ta fara furta kalmar (Innalillahi wa inna ilaihirraji 'un! Allahumma ajirni fi musi bati wa'aklifni khairan minha )"
Fashewa tayi da kuka mai tsuma zuciya, jijjiga kai take tana fadin wash Allah na yaudari kaina na sanyama zuciyata kaunar wanda baisan tana kaunar saba ya Allah ina rokonka ka bani ikon cinye wannan jarrabawa, ya Allah ka sanyaya min radadin da zuciyata keyi a wannan lokaci, ya Allah kasa na dauki komai tamkar ba komai ba ta kara fashewa da kuka.
Sai da tayi kuka mai isarta kafin ta rarrashi zuciyarta. shiru tayi daga bisani tace na dauki dukkan kaddarar da ubangiji ya  dauramin kuma nayi alkawarin sadaukar da dukkan farin cikina ma yar uwata Amal. tana gama fadin haka ta mike jiki ba kwari ta nufi toilet wanke fuskarta tayi ta dauro alwala ta fara sallan walaha.
Umma dakinta ta shiga ta kira Amal ta kura mata ido kafin tace kinji abinda nake fada miki ko ? da ba'a hada 'aurenki da Majeed ba da wacece zataje America ? kuma na lura 'akwai soyayya matuka tsakaninki da Majeed to ki mayar da hankalinki gareshi domin zamu ci ajikinsa sosai.
Dariyar jin dadi Amal tayi kafin tace na gode sosai Umma ina matukar sonki kuma ina 'alfahari da samunki a matsayin mahaifiya a gareni.
Murmushi Umma tayi kafin ta ce kinga shawarar Aunty safiyya ta fara 'amfani ko ? Amal ta ce na gani sosai ma. To daga yau ki fara 'amfani da dukkan abinda na fada miki kina jina ko ? 
Amal ta ce naji zan dauki shawarar Aunty safiyya 'amma bazan taba wulakanta Mommy da y'ar uwata ba.
Ta'be baki Umma tayi kafin ta ce ba matsala 'amma nafi tsammanin daa sannu zaki fahimci abinda na fahimta.
Shiru Amal tayi daga bisani ta ce Umma bari naje na kwanta sbd na gaji sosai. gama fadar haka keda wuya ta nufi kofar fita.
Dakin Mee'ad ta nufa tayi knocking kafin ta tura kofar ta shiga sallah ta samu Mee'ad din keyi bata wani bata lokaci ba ta fita daga daki tana cewa nasan halin sallanki ba yanzu zaki idar ba, dan haka nikam nayi nan.
Hajiya Hindu ce zaune a falon Mommy suna firar yaushe gamo domin sun kwana biyu basuga juna ba Hajiya Hindu ta dubi Mommy kafin tace d'iyata yaushe zakije kasarku ne ? naga kin kwana biyu bakikai musu ziyara ba murmushi Mommy tayi kafin tace Hajiyar mu inason zuwa karshen wannan shekarar amma tinda an saka ranar auren dan dakina na fasa zuwa sai bayan anyi auren.
Murmushin jin dadi Hajiya Hindun tayi kafin ta dubi Mommy cike da kulawa ta ce Fateema wai mi yake damun kine tin lokacin da na shigo gidan nan na lura kwata ~ kwata bakya cikin walwala. dukar dakai Mommy tayi kafin tace laah Hajiyarmu ba komai kawai banijin dadi sosai ne a y'an kwanakin nan.
Ajiyar zuciya Hajiya Hindu tayi kafin ta ce nasan bazaki ta'ba fadamin gasakiya ba ' amma inaso ki kwantar da hankalinki ki kuma koyi kawaici akan kowani irin lamari nasan kinada wadannan halayyen kawai ina kara baki shawara da ki kara hakuri akan nadane kawai.
"Murmushi kawai Mommy tayi bata kara cewa komai ba. Hajiya Hindu tayi mata fada sosai akan rayuwa, sbd ta tsikayi maganganu da yawa ' a bakin larai mai aikin gidan musamman takaima Hajiya Hindu ziyara sbd ta sanar da ita irin abinda Hajiya Suuwaiba wato Umma take yima Mommy a yan kwanakin nan.
Hajiya Hindu bataji dadin hakan ba wannan dalilin ne ya sanya take kara bama Mommyn hakuri.
Hira suka sha sosai kafin Sirikartata ta tafi.
Majeed ne kwance bisa gado sai dannan waya yake kallon pictures din da suka dauka da kannen nasa yake kallo sai murmushi yake zooming din hotonsu yayi ya kyalkyale da daria kafin ya sauka daga gallery yayi dialing number Mee'ad.
Da sallama ta daga wayar kafin tace Yaya barka da dare Murmushi yayi kafin yace barka dai Kawata ya kk ? yau ban ganki a cikin gida ba har na dawo na kwanta. shiru Mee'ad tayi kafin tace yauna yini da ciwon kaine.
Ayyah sorry My best friend nayi miss dinki sosai, murmushi Mee'ad din tayi kafin ta ce ni kuma banyi wani miss dinka ba.
"Murmushi yayi kafin ya ce albishirinki "
" Ta ce goro "
" Goro fari ko jaa "
" Fari tass kamar kai "
Murmushi ya karayi kafin yace na cika miki wani form na kara kwarewa 'akan computer a garin mu.
Wow na gode sosai Yaya Allah ya saka da mafificin alkhairi.
Murmushi yayi kafin yace Ameen. kinga idan kin gama exams sai kije ki fara kafin ku koma school din ko ?
Ta ce ba matsala na gode sosai, tana gama fadin haka tace mukwana lfy. ta katse wayar ba tare da ta jira jin abinda zaice ba.
Bin wayar yayi da kallo kafin yace Mee'ad ina jin sunanki har cikin zuciya da jinin jikina komi ya janyo hakan ?.
Mai karatu biyoni kasha labari

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow