Gwamnatin Zamfara ta amince da daukar malamai 2,000 aiki

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da daukar karin malamai 2,000 aiki a makarantun jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin wani taron majalisar zartarwa a gidan gwamnati dake Gusau babban birnin jihar.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Idris, ya fitar, ta bayyana cewa shirin daukar malaman yana cika wasu alkawuran da aka dauka a lokacin yakin neman zaben gwamna.
Sanarwar ta kara da cewa ilimi, wanda ke zama na biyu a jerin ayyukan gwamnati, ya samu kulawa sosai kuma tuni ya samar da sakamakon da ake bukata a karkashin gwamnatin.
Daga Abbakar Aleeyu Anache.