El-Rufai ga Bwala: Ko ina gwamnatin Tinubu sai na soke ta idan an yi ba daidai ba

Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan jihar Kaduna, ya yi wa Daniel Bwala, mashawarci na musamman kan harkokin siyasa ga shugaban kasa Bola Tinubu wani martani.
A ranar Talata el-Rufai ya soki jam’iyyar APC mai mulki da “baudewa daga ainihin manufofinta”, inda ya kara da cewa ya dawo daga rakiyar da jam’iyyarsa tasa ta siyasa.
Da ya ke mayar da martani ga el-Rufai, Bwala ya tambayi tsohon ministan babban birnin tarayya (FCT) ko ra’ayinsa akan jam’iyyar APC zai sha bamban idan da ace ya na cikin majalisar ministocin Tinubu.
A martanin da ya mayar wa Bwala a wani sako da ya wallafa a shafin sa na X a yau Alhamis, el-Rufai ya ce "ko a gwamnatin Tinubu na ke, zan ce ko kuma in yi haka kan abin da ke faruwa a jam’iyyar da da ni aka kafa ta, da kuma gwamnatin da ta ke mulki a ƙarƙashin ta.
"Zan yi magana ta sirri da wadanda abin ya shafa, sannan na fito fili idan ba a dauki matakin gyara ba,” jigon na APC ya kara da cewa.
El-Rufai ya ce ya shaida wa Tinubu cewa ba shi da sha’awar wani matsayi a gwamnatinsa