Daga Awwal Umar Kontagora, Minna.
Dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana cewar maganar rashin kudi a Nijeriya da gwamnati ke ikirari kawai rashin kwarewar masu mulki ne, domin kasar nan na da arzikin da ba sai an fita a na neman yadda za a yi. Ba gaskiya ba ne, kasar nan tana da arzikin da za a iya saita komai ta yadda za a samu walwala da cigaba.
Sanatan ya bayyana hakan ne ga manema labarai bayan ziyarar kwana daya da ya kawo a jihar Neja da yayan jam'iyyarsa.
Kwankwaso wanda ya sha alwashin kawo matsalar tsaro da ke addabar kasar nan, a cewar sa muddin aka horar da jami'an tsaro yadda ya dace, kuma aka samar masu da kayan aiki suna da kwarewar da zasu iya tunkarar duk wani kalubalen tsaro da ke addabar kasar.
Kasar da ke da arzikin da yan kasa zasu samu walwala, amma rashin sanin makaman aiki yasa dukkanin yan kasa sun zama mabukata, idan ana maganar mabukata a kasar nan kowa mabukaci ne domin yau duk magidancin da ya wayi gari bai da abinda daukar nauyin iyalinsa shi ma ya zama mabukaci, saboda muna da shirye shirye da kudurorin da za mu samar da walwala da cigaba ga yan kasa.
Kullun ana fada mana ana aiki, amma yau ko babbar hanyar minna zuwa suleja kawai ya isa ya nuna ma cewar ba da gaske ake yi ba. " Mun samu labarin kusan dukkanin kusurwowin jihar nan abin magana daya ce, ba sashin da ke da lafiyayyen hanyar da matafiyi zai bi ba tare da fargaba ba. Ga matsalar tsalar tsaro na garkuwa da jama'a, wanda al'ummar karkara mun samu labarin mafi yawa sun zama yan gudun hijira, noman da suka gada suka dogara akai yau yafi karfin su, wanda tilas mu yi aiki tare wajen samar da sabuwar Nijeriya.
Sanata Kwankwaso, ya sha alwashin muddin aka ba shi dama a zaben 2023 zai tabbatar ya fitar da kitse daga wuta ta yadda za a ceto kasar nan daga halin da take ciki.
" Dukkanin yan takarkarun da ke neman shugabancin kasar nan, sun taba rika wani abu, ya kamata jama'a su tsaya su yi dubi ga dukkanin yan takarar su dubi wanda ya taba yin wani abu na cigaba, ba wanda zai yi alkawalin in yaci zabe ba. Abin tambaya wani matsayi ka rika, kuma me ka yi wa al'ummar ka da in ka zo zaka iya dorawa dan kasa ta anfana".