Mun Fito Da Hanyar Zaburar Da Ma'aika Ne Don Inganta Aikin Gwamnati---Barista Sa'adatu Yanusa

Mun Fito Da Hanyar Zaburar Da Ma'aika Ne Don Inganta Aikin Gwamnati---Barista Sa'adatu Yanusa
Mai baiwa Gwamnan Sakkwato shawara kan yaki da fatara a jihar Sakkwato Barista Sa'adatu Yanusa Muhammad ta fito da wasu hanyoyi da za su taimaki aikin gwamnati a jihar Sakkwato don ganin an samu cigaba a kokarin da gwamnatin Dakta Ahmad Aliyu Sokoto take yi na dawo da martabar aiki a jiha.
Barista Sa'adatu Yanusa a wurin taron karramawa da kungiyar Matasan Arewa suka yi mata a ofishinta a satin da ya gabata yayin da take tattaunawa da ma'aikatanta a hobbasar da take yi na ganin sun cigaba da sadaukarwa da bayar da goyon baya ga jagorancin Gwamna Ahead Aliyu ganin yanda yake nunawa ma'aikatan gwamnati kulawa tun sanda ya karbi ragamar mulkin jihar Sakkwato.
A wurin zaman Mai baiwa Gwamnan shawara ta godewa ma'aikatanta kan jajircewarsu ga aiki in da ta jawo hankalinsu ga yin aiki cikin hadin Kai Wanda hakan kawai zai sa a samu cigaba ga mutanen jiha. Ta nuna matukar bukatar sadaukarwa don ganin an rage radadin talauci in aka samu goyon baya ga  shiraruwan da Mai girma Gwamna ya fito da su.
Barista Sa'adatu ta jawo hankalin ma'aikata ganin yanda Gwamna ya yi masu goma ta arziki yakamata su kara dage damtse don ginin an inganta rayuwar al'ummar jiha, don haka su zama masu tsayin daka da amfani da basira da zimmar kawo abubuwan da za su kawar da talauci a cikin al'umma.
Barista ta sanar da cigaban da hukumar ta samar waton na'urar tantance zuwan ma'aikata aiki, za ta rika aiki a lokacin aiki don kididdige masu zuwa da wadanda ke wasa da aiki, "wannan tsari zai samar da rikon amana da kula da ma'aikata yanda ya dace".
"A cikin wannnan tsarin akwai bukatar duka ma'aikatanmu su yi rijista da Sabon tsarin don samar da tantancewa guda, fasahar zamani ba wai kawai za ta bunkasa hukumar ba ne haka ma za a samu aminci da zai karfafa aikin da ake yi,"Kalmomin Barista.
Ta nemi a cigaba da  goyon baya ga shiraruwan gwamnati don ganin bukatar Gwamna ta tsamo mutanen jiha daga cikin talauci ta tabbata.