Maganar Da Ake Yaɗawa Zan Bar PDP A Jira A Gani----Manir Ɗan'iya

Maganar Da Ake Yaɗawa Zan Bar PDP A Jira A Gani----Manir Ɗan'iya

Mataimakin gwamnan Sakkwato Manir Muhammad Dan'iya ya musanta maganar da ake yaɗawa a jihar Sakkwato cewa zai bar jam'iyarsa ta PDP zuwa APC a kakar zaɓen 2023.
Mataimakin gwamnan a hirarsa da manema labarai bayan kammala taron masu ruwa da tsaki na jam'iyarsu a Otal na Ginginya yau in da aka zauna da ƙaramar hukumar Silame, wanda shi ne karon farko da ya halarci taron tun da aka fara a satin da ya gabata.
Manir ya ce "yaushe zan sauya sheƙa, a jira a gani," a cewarsa.
Tun bayan kammala zaɓen fitar da gwani na PDP ake ganin kamar Ɗan'iya zai ɗauki matakin sauya sheƙa saboda bai samu nasarar ba shi tikitin takarar Gwamna ba.
Jita-jitar ta yi ƙarfi sosai kan wasu malamomi da aka riƙa gani, sai gashi yanzu ya tanka ya ce a jira a gani, kalma ce mai harshen damo dake nufin matakin da zai ɗauka za a ganshi a gaba kan sauyin ko akasin haka.