Gwamnan APC a Arewa Na Shirin Komawa PDP?

Gwamnan APC a Arewa Na Shirin Komawa PDP?

 
Gwamnatin jihar kogi ta yi magana kan cece-kuce da ake yi bayan ganin Gwamna Usman Ododo a taron PDP. 
Gwamnatin ta ce har zuwa yanzu Gwamna Ododo dan jam'iyar APC ne kuma babu abin da zai fitar da shi a cikinta. 
Gwamnati ta ƙaryata cewa Ododo zai koma PDP 
Kwamishinan yada labarai a jihar, Kingsley Fanwo shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a yau Asabar 24 ga watan Agustan 2024, cewar Punch. 
Fanwo ya ce Ododo ba shi da wani shiri na komawa jam'iyyar PDP inda ya ce kawai rashin kwarewar masu yada labarai ne. 
"Mun samu rahoton da ke yada cewa Gwamna Ododo na shirin komawa jam'iyyar PDP daga APC." 
"Babu kamshin gaskiya a cikin labarin da ake yadawa, mu ne muke da damar yada labarin gaskiya kuma wanda ya dace."
"Masu yada wannan labari ba su gama fita daga gigitar da suka yi ba bayan rasa nasara a Kotun Koli."  
Kingsley Fanwo Musabbabin haɗuwar Ododo da gwamnonin PDP Gwamnatin ta ce musabbabin ganin Gwamna Ododo a cikin gwamnonin PDP ya halarci daurin auren yar Gwamna Agbu Kefas ne na jihar Taraba.