Macen da bata taɓa saduwa da namiji ba kawai ya kamata a riƙa baiwa sadaki - Omokri 

Macen da bata taɓa saduwa da namiji ba kawai ya kamata a riƙa baiwa sadaki - Omokri 

Tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara, Reno Omokri, ya ce ya kamata a daina biyan sadaki ga matar da ta taɓa saduwa da namiji, yana mai bayyana cewa hakan ya zama wata hanya ta tilastawa mutane biyan kudi ba bisa ka’ida ba.

A wani dogon sakonsa da ya wallafa a shafinsa na X, Omokri ya bayyana cewa a al’adun Afirka da Yahudawa, sadaki na nufin kudin da namiji ke biya wa iyayen budurwa, kuma hakan na da tushe a cikin Littafi Mai Tsarki, musamman a Fitowa 22:17.

Ya bayyana bambanci tsakanin "kayan Aure" da "sadaki", inda ya ce kayan daki dukiyar iyaye ne ke bai wa ’yarsu a ranar aurenta, amma sadaki na nufin kudi ko dukiya da ango ke biya don auren budurwa.

Omokri ya soki yadda wasu kabilun Afirka ke bukatar sadaki mai yawa ga mata da ba budurwa ba, yana mai cewa hakan ya zama cin zarafi da kuskuren al’ada.

Ya kuma ce a cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar "amarya" tana nufin budurwa ne kawai, yana ba da misalai da dama don kare wannan matsayi.

A karshe, Omokri ya ce aure irin na fararen fata ba al’adar Afirka ba ce kuma ba addinin Kirista ba ne, yana mai bukatar mutane su fahimci asalin al’adunsu domin hana rugujewar tarbiyya.