LISSAFIN ƘADDARA: Fita Ta 9&10

A falo sukayiwa kansu masauki in da suka samu Hajiya Nana, Khadija da Ameenatuh sukayi hanyar dakinsu sai dai tunkan suyi nisa Abban Hammad ya dakatar da su yana mai nuna musu gurin zama suka koma suka zauna,

LISSAFIN ƘADDARA: Fita Ta 9&10

LISSAFIN ƘADDARA


ZAINAB SULAIMAN
       (Autar Baba)

DEDICATED TO SHAMSIYYA USMAN MANGA



P 9&10

Idanuwansu ne ya sarƙe da juna jikin Umma kuwa ɓari kawai yake ganin wanda ke gabanta a yanzu,gaba ɗaya sai ƴan gurin suka zama ƴan kallo da son jin wane wannan da alamu suka gama tabbatarwa Umma ta sanshi,tsaki Hammad yayi ya juya dan komawa part dinsu sai kuma muryar mahaifinsa da ya jiyo yasa ya ɗan dakata da niyar tafiyar"Bawan Allah daga ina haka zaka shigo gidan mutane ka tayar musu da hankali,ba wani ne man izini zaka shigo gidan matan aure"Abban Hammad ya ƙarasa maganar cikin nutsuwa da tsare gida,hararar da mutumin ya waysa masace tasashi sakin baki cike da mamaki yake kallon mutumin kafin cikin gadara yace"lokacin da kuka ɗaukarmun mata kun nemin izinina,ai dole ka ganni cikin gidanka ba neman izini saboda matan aure da kake tunƙaho dasu a gidan ai har da tawa matar"kallon Umma yayi cike da iskanci ya sheƙe da dariya kan ya gumtse  yace "Maryam banso horon da na miki ya tsaya iya haka ba naso kin shiga uƙuba sanadiyyar tukuicin ƙauna,kinsan kin saɓa alƙawari domin da nasan kema tukuicin da zaki bani na haihuwar ƴaƴa mata da tun farko ban aureki ba,zaki bani girin zama muyi magana ko na buɗeta anan?" ya ƙarasa maganar cike da shaƙiyanci, kallon banza Abban Hammad ya watsa masa dan shi sai yanzu ya lura ma da shigar mahaukantan dake tattare dashi dan kuwa wanda ko ba mahaukaci bane to giyar mugun talauci na ɗawainiya da shi,juyawa yayi ya kai dubansa ga Umma yana son yaji ta bakinta sai dai yadda ƙirjinsa ke lugudene yasa idanunsa kasa ɗaukewa  akan Umma,gabansa ne yaci gaba dafaɗuwa bakinsa ya kasa rufuwa shidai baisanta ba bai kuma taɓa ganinta ba tabbas Allah buwayi gagara misali zallah kamar Umma da Mahaifiyarsa ne duk yasashi ruɗewa sai dai yasan ba abun mamaki bane Allah zaiyi wanda yafi haka ma hakan yasa cike da mutuwar jiki ya bata umarnin keɓewa da mutumin shi kuma yaja Hammad dasu Ameenatuh suka koma ciki,

A falo sukayiwa kansu masauki in da suka samu Hajiya Nana, Khadija da Ameenatuh sukayi hanyar dakinsu sai dai tunkan suyi nisa Abban Hammad ya dakatar da su yana mai nuna musu gurin zama suka koma suka zauna,

A ɓangaren Umma kuwa ta kasa gaba ta kasa baya dan haka ta tsaya guri guda idanuwanta na fitar da kwalla masu zafi matsowa sosai mutumin yayi yana murmushi yace "Maryam   naso na rayu da ke cikin aminci sai dai taurin kanki yasa kika gaza fahimta ta,bama wannan ba nazo ne dan karɓar a jiyata lallai na yaba miki Maryama kin iya raino so nake ki bani Babbar 'yarki dan nayi mata miji a bokina ya gani kuma ya yaba "yadda kasan dutse yake magana ita Umma zuciyarta ce kawai ke aiki amma gangar jikinta da hankalinta ba a tare suke da ita ba kalamar innalillahi wa'inna ilaihiraji'un kawai take maimaitawa,


A can cikin gidan kuwa Abba ne ya kallesu yace"shi wannan din kunsan shi ne?"Ameenatu ce tayi juriya wajen cewa"eh mun sanshi a company da muke aikin ƙaro company abokinsa ne kuma shima company sa na citta yana gurin sai naji ance yayi gobara kwanaki" a jiyar zuciya ya sauke kafun yace "ko kunsan mahaifinku" sai da sukayi jum kafun a tare su girgiza kai alamu a'a "Umma tace tun ranar da aka haifi Khadija itama bata kuma ganinsa ba" tsaki Abba ya ja a fili ya tashi yayi ɓangaren iyayensa.

"ba ki ce komai ba kin ta farantamun rai kinsan kukan maci amana akwai dadi" wata wawiyar ajiyar zuciya ta sauke kan da dawo da dubanta gareshi tace "ashe kana da a jiya tattare da ni?lallai Ishaq idonka ba kwallai a cikinsa baka da imani baka da tausayi,ba kuma ina kuka ne saboda farin cikinka ko baƙin cikinka ba ina kuka ne saboda kasancewarka uban ƴaƴana da basuji ba basu gani ba ƙaddara take neman yagalgala rayuwarsu""hmm Maryama kenan wuyanki ya  isa yanka kin fara maidamun magana kinyi abu kuma yazo yana damunki karki manta fa mahaifinki a gabana ya furtabaya sona da ke kema kuma a gabana kika furta kinasona kuma a gaban mahaifin naki dan haka ba wata ƙaddara da take bin ƴaƴanki face haƙƙin iyayenki dan haka in kinaso tarihi ya maimaita kansa ki hana ƴarki auren zaɓina ni dai ubansu ne kamar yadda kika faɗa a baya ba'a canzawa tuwo suna"ya juya cike da jindadi dan yasan ya baƙanta mata sai kuma ya juyo yace"am za'a ɗaura auren ranar juma'a a masallaci Tudun wada sannan kema a ranar zaki koma ɗakinki dan nima na gaji da zaman ɓuya da muke".....

Ayi sharhi ayi share in naga canji mai yiyuwar anjima kuga sabon update,

Autar Baba ce