Kwamitin bincike na gwamnatin Sokoto ya baiwa Manir Dan'iya da Yusuf Suleiman dama ta ƙarshe

Kwamitin bincike na gwamnatin Sokoto ya baiwa Manir Dan'iya da Yusuf Suleiman dama ta ƙarshe

Kwamitin bincike da gwamnatin Sakkwato ta kafa ya  gargaɗi tsohon mataimakin gwamna Alhaji Manir Muhammad Dan'iya a karo na karshe  da ya  bayyana a gabanta  a zaman da za ta sake yi 22 ga watan Mayun 2024.

Haka ma kwamitin ya tura irin wannan gargadin ga tsohon babban daraktan kamfen jam'iyar PDP a zaben 2023 Alhaji Yusuf Suleiman Ɗan Amar Sokoto.

A cewar kwamitin dukkan su biyu akwai bayanin da ake so su yi a gaban kwamitin kan wani Memo 007  da ke gaban kwamitin.

Lauya Dan'iya, Barista Nuhu Adamu ya nemi a sanya masu wata rana abin da shugaban MU'AZU Pindiga   ya aminta da hakan.

Ya umarci 'yan sanda su lika takardar gayyata a jikin ginar Dan'amar Sokoto in har ba a same shi gida ba.