Duk wahalar da cire tallafin Man Fetur ya jawo Atiku Bagudu ya goyi bayan matakin

Duk wahalar da cire tallafin Man Fetur ya jawo Atiku Bagudu ya goyi bayan matakin
 

Ministan kasafi da tsare-tsare, Atiku Bagudu ya yabawa matakan da Bola Tinubu ya dauka a Najeriya. 

Bagudu ya ce matakin cire tallafin mai da Tinubu ya yi, ya aiwatar da abin da ya kamata a yi shekaru da dama da suka wuce.
Tsohon dan Majalisar Tarayya ya ce abin da sauran shugabanni da 'yan takara suke son yi ne suka gagara Tinubu ya aiwatar a lokaci guda. 
Tsohon gwamnan Kebbi ya yabawa Tinubu kan irin kokarin da ya yi a cikin watanni 11 kacal da ya yi a kan mulki, cewar Premium Times. 
"Tun farko Tinubu ya nuna jarumta wurin daukar matakan da sauran 'yan takara ke son dauka wanda shi ne cire tallafin mai." "Wannan ba lamari ba ne na zarge-zarge da neman wanda za a daurawa laifi, Tinubu ya dauki matakin ne saboda bai son zargin kowa." 
"Amma wasu suna jinkirin daukar matakin da sauran tsare-tsare wanda ya kamata a dauka shekaru aru-aru da suka gabata."