Kotu ta umarci Sarakunan Kano Da Aka Tuɓe Su Mayar Da Kayan Gwamnati Da Ke Hannunsu

Kotu ta umarci Sarakunan Kano Da Aka Tuɓe Su Mayar Da Kayan Gwamnati Da Ke Hannunsu
 

Babbar Kotun Kano ta umarci sarakunan masarautun jihar da aka tube da su mayar mata da duk wani kaya mallakar gwamnati da ke hannunsu.

 

Da take yanke hukuncin, alkalin kotun, Mai sharia Amina Adamu Aliyu ta tabbatar da ikon da Majalisar Dokokin Jihar Kano take da shi ma yin doka.

Alkalin ta ci gaba da cewa gyaran dokar masaraun jihar da majalisar ta yi yana kan daidai, hakazalika sa hannun da Gwamna Abba Kabir ya yi a kan dokar yana kan daidai.

Sai dai kotun ta ki amincewa da rokon masu kara na cewa a fitar da Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero daga Fadar Nassarawa.