Jam’iyar APC shiyyar Arewa ta tsakiya ta yi gargadi kan shirin da wasu kungiyoyi da daidaikun mutane keyi na shirya zanga-zangar adawa da gwamnatin shugaba Bola Tinubu a fadin kasar.
Taron ya ce irin wannan matakin ba za ta yi tasiri ba zai yi kuma illa ga ci gaban kasar a halin yanzu, inda ta yi kira ga masu shirya Zanga zangar da su sake tunani, su kuma ja da baya.
Shugsban muryar yan jamiyyar APC a yankin, Saleh Mandung Zazzaga, a taron manema labarai a Jos a yau Litinin ya yi kira ga masu shirya zan-zangar da su yi duba na tsanaki a kan yanayin da kasar ke ciki kafin su yanke hukunci.
A cewar sa, Tinubu na iya kokarin san a wajen seta Nijeriya, inda ya yi kira gay an kasar da su mara masa baya a maimakon yi wa gwamnatinsa zagon-kasa da sunan zanga-zanga.





