2023: Tambuwal Ya Kashe Miliyoyin Kudade Ga Hayar Jirgin Sama A Rangadin Jihohi 20

2023: Tambuwal Ya Kashe Miliyoyin Kudade Ga Hayar Jirgin Sama A Rangadin Jihohi 20

Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal yana cikin ‘yan takarar shugaban kasar Nijeriya  38 a jam’iyar PDP da APC da suka   kashe miliyoyin kudade ga jirgin sama a wurin rangadin neman kuri’ar wakillan jam’iya.

Tambuwal har wayau yana cikin gwamnoni 9 dake neman a tsayar da su takarar, shi da Gwamnan Rivers Wike sun fi sauran gwamnonin kai ziyarar in da kowanensu ya tafi jiha 20 sabanin sauran gwamnonin kamar yadda jaridar Daily Trust ta kawo.

A halin da ake ciki in  za ka dauki jirgin haya kudinsa sama da miliya hudu ne zuwa miliyan 5.8 a kowace awa ya danganta da girman jirgin da mutum ya yi haya.

Wani matukin jirgi  ya ce abin zai fi haka in mutum ya dauki jirgin alfarma a kalla mai daukar mutum 11 har sama da  13.

Haka ma ma’aikatan jirgi da sauran kaya ana biyan Dala 3,000 a awa daya bayan ka biya kudin jirgi  ya dangnta da jirgin da mutum ya dauka, in ya sauka a filin jirgi kan ko za ka tafi ka dawo ne ko kafiya ce kawai.