Sabuwar Cuta Ta Bulla a Sokoto Har Ta Kama Mutum 71

Sabuwar Cuta Ta Bulla a Sokoto Har Ta Kama Mutum 71
Hukumar NCDC mai yaki da cutuka masu yaduwa a Najeriya ta tabbatar da bullar cutar zazzabin Dangue a jihar Sokoto a ranar Asabar, 16 ga watan Disamba.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na yanar gizo, NCDC ta ce an gano bullar cutar ne a watan Nuwamban 2023 
Sanarwar dauke da sa hannun Darakta Janar na NCDC, Ifedayo Adetifa, ta bayyana cewa zuwa yanzu, akwai mutum 71 da ake zargin suna dauke da ita, an tabbatar da 13, kuma ba a samu wanda ya mutu ba a jihar. 
 Masu dauke da cutar sun fito ne daga kananan hukumomi uku - Sokoto ta Kudu (60), Wamako (uku) sai Dange Shuni (daya). Hukumar ta ce a halin da ake ciki yanzu barazanar barkewar cutar ta dengue yana a tsaka-tsaki dangane da kimanta hadarin da ke tattare da shi. 
Legit ta rahoto cewa zazzabin Dengue cuta ce mai radadi, zazzabin cizon sauro mai zafi wanda daya bisa hudu na kwayoyin Dengue ke haifar da shi. 
Yana iya zama mai barazana ga rai a cikin yan sa'o'i kadan kuma sau da yawa yana bukatar kulawa a asibiti.