Ciwon sanyi da hanyoyin magance su a jikin mutum 

Ciwon sanyi da hanyoyin magance su a jikin mutum 

SHIN MEKE KAWO CIWON SANYI (INFECTION)

Ciwon sanyi wato (infection) ciwone wanda yazama ruwan dare a tsakanin al'umma. ciwone wanda yakeda matukar hadari shiyasa akesan a dauka masa mataki cikin gaggawa.

Ciwone wanda yakeda saurin yaduwa sosai tsakanin jama'a kuma ta hanyoyi daban-daban.

Hasalima idan ba'a dauka mataki da wuri ba yakan iya hana haihuwa kuma anfi daukarsa ta hanyar jima'i.

MEKE KAWO CIWON SANYI

Kwayoyin cuta da dama suna haddasa wannan cutar amma kwayar cutar bacteria sune kan gaba da kuma tasiri wajen kawo wannan cuta, kwayar cutar bacteria kamar irinsu:

• Neissera gonorrhea
• Bacterial vaginosis
• Escherichia coli(ecoli)
• Traponema pallidum

SHIN TA WACE HANYA AKE DAUKAR CIWON

Kamar yanda na ambata a farko a ana daukarsa ta hanyoyi daban-daban amma mafi yawan lokuta amfi daukarsa ta hanyar jima'i.

Sauran hanyoyin da ake daukarsa sun hada da

• Amfani da bandaki(toilet) marasa tsafta
• wanke gaba da sabulu(Soap)
• Shan magani ba bisa ka'ida ba
• Rashin tsaftace muhalli
• Yin amfani da magungunan da ake sakawa a gaba(Vagina)
• Yin tsalki da ruwan dimi na tsawon lokaci

YA ALAMOMİN WANNAN CIWON SUKE

Anan zan fara da mata saboda sune sukafi fama da wannan cutar alamomin gasu kamar haka:-

• Fitar wasu ruwa a gaban mace(discharge) musamman kalar daurawa wato yellow
• Jin ciwo lokacin al'ada
• Jin ciwo lokacin saduwa
• Yawan fitsari(A wasu lokuta)
• Fitar wasu ruwa a gabanki masu wari
• Fitar quraje a gabanki
• Fitar jini bayan saduwa
• Qaiqayin gaba
• Zubewar gashin mara
• Bushewar gaba
• Warin gaba
• Rikecewar al'ada
• Yawan zubewar ciki
• Yawan ciwon mara

MAZA kuma alamomin sune kamar haka:-

• Fitowar wasu ruwa a gabanka kafin ko bayan fitsari
• Yawan fitsari a wasu lokuta
• Jin ciwo yayin fitsari
• Daukewar Sha'awa
• Ciwo a matse-matsi
• Fitar kuraje a gaba
• Jin ciwo lokacin jima'i
• Qabewar kaciyar Namiji(Balinitis)
• Qanqantar gaba
• Kumburar matse-matsi
• Rashin iya gamsar da iyali
• Saurin inzali

SHIN ANA WARKEWA DAGA WANNAN CUTAR KUMA TAYA ZAN IYA KARE KAINA DA ITA

Eh sosai ma kuwa muddin ka/ki fuskanci wasu daga cikin alamomin da na zayyana a sama, to yanada kyau kayi gaggawar garzayawa a assibiti mafi kusa dakai domin bincika da kuma tabbatarwa sannan a daura ka bisa magungunan da suka dace.

HANYOYIN KARIYA DAGA CUTAR GA KADAN DAGA CIKI

• Tsafatace muhalli
• Tsaftace Bandaki kapin da kuma bayan amfani
• Ki dinga saka pant na cotton kawai banda na roba
• Barin shiga ban dakin kan hanya batare da kasaka ruwa ba
• Ki daina wanke gabanki da sabulu(Soap)
• Daina amfani da duk maganin da ake sakawa a gaba
• A daina matse gaba(Vaginal tighting)
• A kula da tsaftar dan kanfai 

RASHIN DAUKAR MATAKI AKAN WANNAN CİWON YAKA IYA HAIFARDA

• Rashin haihuwa
• Kashe aure
• Lalata gaban mace
• Lalata gaban namiji
• A karo maki kishiya

Daga karshe kuma dan ALLAH gareku,  uwayenmu, Qannenmu, yannenmu da kuma yan uwanmu Mata ku daina wanke gabanku(Vagina) da sabulu(soap).

Saboda yanda ALLAH ya halicci gaban mace wajen is Acidic in nature ita kuma sabulu is alkaline in nature, yin amfani da sabulu yakanyi neutralizing Acid dinda ke wajen, idan kuma akayi neutralizing acid din to kowace cuta zata iya shiga.

ALLAH yasa mudace kuma yakaremu da cutukan zamani.

Nr. Suleiman Muhammad 
(RN). Health Educator.