Rashin Girmama Shugabanci: Wata Jihar Arewa, Gwamna da Mataimaki Sun Tafi Hajji

Rashin Girmama Shugabanci: Wata Jihar Arewa, Gwamna da Mataimaki Sun Tafi Hajji

 

Gwamna Mohammed Umaru Bago na jihar Neja; mataimakinsa, Yakubu Garba; da kuma kakakin majalisar jihar, Barista Abdulmalik Sarkin-Daji duk sun tafi aikin Hajji. 

Haka kuma, da dama daga cikin kwamishinoni da wasu ‘yan majalisar jihar su ma sun tafi aikin hajjin, lamarin da wasu mazauna jihar da jam'iyyar PDP suka yi Allah wadai. 
Babu wani tabbaci da aka samu kan ko gwamnan ya mika mulki ga wani a hukumance kafin ya tafi aikin hajjin, in ji rahoton jaridar Daily Trust.
An ce jama'ar jihar na ganin gwamnati da 'yan majalisun sun yi watsi da su, duba da irin abubuwan da suka faru da suka yi sanadin mutuwar mutane da dama. 
Tafiyar gwamnan da wasu manyan jagororin jihar ta biyo bayan wani hatsarin da ya afku a ramin hakar ma'adinai da ya binne mutane da dama. 
Majiyoyi a Minna sun ce sakataren gwamnatin jihar (SSG), Alhaji Abubakar Usman ne ke gudanar da ayyukan gwamnati tun ranar Litinin. 
Sai dai babu wata sanarwa da gwamnatin jihar ta ba kafafen yada labarai da sadarwa a hukumance ba. Duk wani yunkuri na tuntubar ofishin SSG ya ci tura.