Dalibar FGC Yauri da Aka Sace Ta Haihu a Hannun ‘Yan Bindiga 

Dalibar FGC Yauri da Aka Sace Ta Haihu a Hannun ‘Yan Bindiga 


Matashiyar budurwa mai shekaru 16 daga cikin daliban kwalejin tarayya dake Yauri a jihar Kebbi ta haihu a hannun ‘yan bindigan da suka yi garkuwa da su, jaridar PRNigeria ta rahoto hakan. 

Dalibar tana daya daga cikin wadanda ‘yan bindigan suka sace a farmakin da suka kai makarantar cikin watan Yunin 2021. 
Kamar yadda PRNigeria ta bayyana a ranar Lahadi, majiyoyi sun ce dalibar wacce ba a tabbatar da sunanta ba ta haifa yaro namiji a sansanin wadanda suka sace su a daji. 
Daya daga cikin majiyoyin sun ce, iyayen 11 daga cikin ‘yan matan dake hannun masu garkuwa da mutanen sun bayyana damuwarsu ganin cewa duk da an biya kudin fansa kuma an yi musayar fursunoni, har yanzu ba a saki ‘ya’yansu ba. 
“A yayin da Atiku Bagudu, Gwamnan jihar Kebbi ya soke cinikayya da ‘yan bindigan wadanda suka bukaci kudin fansa, iyayen daliban da aka sace sun hada kudi tare da biyan na fansa domin sako ‘ya’yansu.” - Wata majiya tace. 
“Abun takaici ne yadda ‘yan bindigan suka karba makuden dukiya na fansa kuma suka aurar da wadanda suka sace tare da kin sakinsu.” - Majiyar tace.