Tinubu ya  Mayar da Hidikwatar  Hukumar filayen jiragen sama Legas

Tinubu ya  Mayar da Hidikwatar  Hukumar filayen jiragen sama Legas

 

A ranar Alhamis gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ta dauke wasu sassan  ofishin hukumar filayen jiragen sama ta kasa (FAAN) daga Abuja zuwa Legas. 

Ministan sufurin jiragen sama da sararin samaniya, Festus Keyamo ya sanar da hukuncin dauke ofishin hukumar a ranar Alhamis a wata sanarwa a shafinsa na X.
A shekarar 1976 ne aka kafa hukumar FAAN, amma sake fasalin dokar sufurin jiragen sama a shekarar 1995 ya sa gwamnati ta hade ayyukan hukumar NAA zuwa hukumar FAAN. 
Hukumar na kula da dukkanin filayen jiragen sama mallakin gwamnatin tarayya, kuma an yi mata hedkwatar farko a Legas. 
Sai dai a 2020, Shugaba Buhari ya mayar da ofishin Abuja. Sanarwar Ministan ta ce dauke hedikwatar hukumar daga Abuja zuwa Legas shi ne mafi alkairi ga Najeriya musamman ganin cewa ana hada-hadar kudaden jama'a a ciki. 
Dalilai 4 na dage hedikwatar FAAN daga Abuja zuwa Legas 
1. Rashin ofis ga ma'aikata Ministan ya yi nuni da cewa babu wadatattun ofis ofis ga ma'aikata a hedikwatar da ke Abuja, hakan ya tilasta da yawan ma'aikata suka koma Legas. 
Ya ce tun farko an yi kuskuren maido da hedikwatar hukumar zuwa Abuja, la'akari da cewa babu wani gini guda daya mallakin FAAN wanda zai iya daukar dukkan ma'aikata. 
2. Biyan ma'aikata alawus din DTA Bayan da ma'aikatan suka koma Legas da aiki, hakan ya saka hukumar biyansu kudin alawus din DTA, saboda a hukumance kamar suna aiki ne a wajen ma'aikatar. Ministan ya ce wannan barnatar da kudin jama'a ne kawai, don haka gwanda a mayar da hedikwatar Legas kowa ya huta. 
3. Za a gina hedikwata a Abuja da Legas Ministan ya bayyana cewa akwai shirin da gwamnati ta yi na gina ofishin hukumar a Legas da Abuja da zai wadatar da kowa. 
4. Abuja ko Legas, inda hedikwatar za ta zauna Festus Keyamo ya ce nan gaba idan aka gama gina ofishin hukumar a Legas da Abuja, za a cimma matsaya kan garin da zai zama hedikwata.