Daga Awwal Umar Kontagora, Minna.
A karon farko kungiyar mahaddata Al'kurani ( The Huffazul Qur'an And Scholars Association) ta kasa reshen jihar Neja, ta tallafawa almajirai tamanin da kayan sana'o'in hannu na sama da dubu dari hudu da tamanin.
Da yake jawabi a fadarsa, mai martaba sarkin Minna, Dakta Umar Faruk Bahago ya jawo hankalin masu hannu da shuni da su rika bada tallafi a bangaren addini musamman ganin halin da kasar ta samu kanta na rashin tsaro. Yace wannan shirin na huffazu abin a yaba ne musamman ganin an kaddamar da shirin farko na karfafa guiwar almajirai wajen dogaro da kai, hakan zai taimaka wa shirin gwamnatin jiha na haramta yawon barace baracen almajiran kur'ani a wuraren da gwamnati ta haramta musamman bankuna, mararrabun manyan hanyoyi, hotel da tashoshin mota.
Dakta Faruk, yace lokaci yayi da iyayen yara ya kamata idan zasu kai 'yayansu makarantun allo su rika samar su abubuwan dogaro da kai ba su dogara da bara ba wajen gudanar da rayuwarsu wajen neman ilimin addini.
A na shi bayanin shugaban kungiyar ta jiha, Amb. Abubakar Sadiq Maiturare, yace kungiyar ta shirya bada tallafin ne ga almajirai dan ganin mun kawo saukin yawon bara ga almajiran makarantun tsangaya, duk da cewar ba zasu iya kawo karshen matsalar ba gaba daya ba, amma muna yunkurin kawo sauki da karfafa guiwar almajiran makarantun tsangaya wajen dogaro da sana'a ba yawon bara ba.
Dan haka muna jawo hankalin malaman tsangaya da su kara kaimi wajen hana yawon bara akan manyan hanyoyi, da wasu wuraren da gwamnati ta hana, haka ya kamata malamai su samar da tsarin duk wani almajirin da zai koyi karatun al'kur'ani a tsangayarsu su tabbatar sun koyi wata sana'ar hannu ta yadda zasu iya rike kan su ba sai sun dogara da barace barace ba.
Da yake jinjina ga kokarin kungiyar ta jihar Neja, Kodinetan kungiyar mai kula da arewa ta tsakiya, Amb. Musa Adamu, ya bayyana cewar jihar Neja itace ta farko da ta kirkiro irin wannan aikin cigaban a duk yankin arewa ta tsakiya, don haka muna jinjinawa shugabancin da masarautar Minna da ta karfafa guiwar su.
Yace sakamakon irin halin da mu ke ciki yau rayuwar almajirai na tsaka mai wuya na rashin tsaro, saboda wannan shirin zai taimakawa almajirai dogara da kai da neman ilimi ba tare da kaskanci ba.
Tsangayu arba'in ne daga yankunan kananan hukumomin Paikoro, Chanchaga da Bosso a zabo almajirai tamanin dan fara gwajin da su, inda kungiyar ta bayyana cewar zango na biyu na shirin na kan hanya.
Kayayyakin sana'o'in da aka tallafawa almajiran sun hada da kayan shoe- shiner guda arba'in da suka ci adadin kudi naira dubu dari biyu, sai koba ta kayan adon mata guda arba'in da su ma suka ci jimilar kudi naira dubu dari biyu da arba'in, an dai kashe sama da dubu dari hudu da tamanin ga kayan tallafin.
An gudanar da taron rabon tallafin ne a fadar mai martaba sarkin Minna, Dakta Umar Faruq Bahago, taron ya samu halartar manyan malaman tsangaya, alarammomi da dalibai masu neman ilimin kur'ani mai tsalki.