Sagir Bafarawa Ya Bayyana Gaban Kwamitin Binciken Gwamnatin Tambuwal

Sagir Bafarawa Ya Bayyana Gaban Kwamitin Binciken Gwamnatin Tambuwal

Tsohon Kwamishinan Muhali a Gwamnatin Sanata Aminu Waziri Tambuwal data gabata ya bayyana a Gaban Kwamitin Bincike da Gwamnatin Ahmad Aliyu Sokoto ta kafa don gano badakalar da aka tafka da yin Gwanjon motoci ba bisa ka'ida ba da Kuma yanda aka salwantar da kudin gwamnati.
Alhaji Sagir Bafarawa ya fuskanci Kwamitin in da ya amsa tambayoyin mambobin kwamiti da lauyoyinsa da dana kwamitin.
A cikin tambayoyin da ya karba akwai batun Gwanjon motocin ma'aikatar da aka yi ba bisa ka'ida ba, da maganar kashe kudi cikin son rai.
Alhaji Sagir a karshe ya bayyanawa Kwamitin duk abin da ya yi bai yi ne don ya amfana a kashin kansa ba, sai don jama'a Kuma ya bi ka'ida a wurin aiwatar da lamarin.