Bukin Sallah:Uwargidan Sarkin Kagara Ta Tallafawa Yara Marayu Da Kayan Karatu

Bukin Sallah:Uwargidan Sarkin Kagara Ta Tallafawa Yara Marayu Da Kayan Karatu
Daga Awwal Umar Kontagora a Minna.
Gimbiyar sarkin Kagara, Hajiya Rukayyah Ahmad Garba Attahiru II ta tallafawa yara marayu da suka rasa mahaifan su da kayan karatu a karkashin Taimako Global Foundation.
Tunda farko da yake bayani ga jarida Managarciya, shugaban gidauniyar, Malam Husaini Garba Attahiru, yace ganin irin halin da yara marayu ke ciki na rashin mahaifansu, muka shawarci mai babban daki kan ta shiryawa marayu wani taron da za a nishadantar da su dan cire masu kewar halin da suke ciki, Allah cikin ikonsa ta amince.
Ganin a fada mai martaba, bisa al'adar masarauta kan amshi bakuncin yayan masarauta, kuma a wannan sallar yana kasa mai tsalki, sai muka dacewar shigo da su marayun a fada, dan su kara fahimtar cewar suma yayan masarauta ne, kuma suna ikon shigowa dan gaisawa da uwar marayu.
Abinda Taimako Global Foundation tayi, mun zakulo marayu ne daga sassan mazabu goma na masarautar nan karkashin gidauniyar marayu na kungiyar Izalah, wanda duk mutumin da ya rasa ransa a masarautar nan suna record na yayansa.
Yanzu za mu fara da yara guda dari maza da mata, abinda muka shirya yanzu akwai wasan kacinci kacinci, wanda za mu ware gwaraza a cikin su ayi masu kyauta ta musamman, sannan akwai wasannin motsa jiki da muka shirya, shi ma karrama gwaraza na musamman sannan kuma akwai tallafin kayan karatu ga dukkansu su dari kowa zai ci moriyar wannan tallafin.
Tun bayan nadin mai martaba, mun zo da shiraruwa da dama dan tallafawa al'ummar Kagara, wannan tallafin karatun ita uwar mu, Hajiya Rukayyah Ahmad Garba Attahiru ke daukar nauyinsa, kuma muna da wasu a gaba bayan kammala wannan. Mun kuduri aniyar shajja'a yara marayu ne ta fuskar ilimi da karfafa guiwarsu ta yadda za mu cire masu kewar kadaicin da suke fama da shi.