INA HUJJAR TAKE:Labari Mai Sosa Zuciya, Fita Ta Biyar 

Ai Inna Kande ta zabura zata koma cikin gidan ga alama kuma faɗawa zatai cikin rijiyar yadda ta firgice yasa Musa yin ta maza ya afka gidan kai tsaye ya faɗa cikin rijiyar .

INA HUJJAR TAKE:Labari Mai Sosa Zuciya, Fita Ta Biyar 

      Page 5

 

 

Tana ta sheƙa uban gudu sai littafin ya faɗi ƙasa bata sani ba harta isa gida.

Ko da ta isa gidan da gudu ta faɗa kewaye (banɗaki) tana fitowa ta shiga kwaɗama Inna Kande kira kamar wadda faɗa rijiya.

Inna Kande tana ta sheƙa barcinta hankali kwance ta jiyo ihun da Lantai ke yi ta zabura ta faɗo daga kan gadon tawo waje kai tsaye ta nufi bakin rijiyar tana kiran...

"Lantai ke Lantai ubanwa ne ya samun ke rijiya ?

Na shiga ukuna ni Kande idan Lantai ta mutu ya zan yi ?

Ta fice da gudunta tana kiran mutane su zo su taimaka mata kada Lantai ta  mutu ta bi iyayenta inshiga tara ni Kande."

 

Musa dake zaune yana karatu ƙofar gidansu yaga fitowar Inna Kanden a haukace yasa ya ɗago kanshi don ganin abin da ya biyota .

Domin kamar wani ya biyota haka tsohuwar ta fito da gudu tana kwakwazon ta shiga  ukunta.

 

Nan da nan mutane suka kewayeta ana tambayarta abin da ke faruwa cikin gidan.

Gidan take nunawa tana cewa kada su bari ta bi iyayenta itakam idan Lantai ta mutu ƙauyen zata bari.

 

Lantai kuwa tana ganin yadda Inna Kande ta firgice ta zata cikin rijiya ta faɗa sai abin ya bata dariya, amma jin mutane na cewa a ɗauko kwaranga a shiga a fito da ita da sauri yasa ta sunkuci tsakuwar Inna Kande dake kusa da ita ta jefa cikin rijiyar ta cigaba da kwaɗa kiran sunan Inna Kanden tana "Mun bani mun lalace Inna Kande mutuwa ta zo Inna Kande wayyo Allah."

 

Ai Inna Kande ta zabura zata koma cikin gidan ga alama kuma faɗawa zatai cikin rijiyar yadda ta firgice yasa Musa yin ta maza ya afka gidan kai tsaye ya faɗa cikin rijiyar .

 

Me Lantai zatai inba dariya ba?

 

Ta duƙa tana cewa, "Kai maza ka cirota Musa da ita zamu ƙara da Sallah idan ta mutu naman ya rage auki kenan."

 

Mutane na shigowa suka ga Lantai duƙe gaban rijiya sai cewa take wai a fiddota sai suka juya suka kalli Inna Kande da mamaki a fuskokinsu .

 

Inna Kande na ganin Lantai ta ruga ta rungumeta jikinta tana kuka kamar ranta zai fita.

Lantai tai luf tana kallon mutane da mamaki yasa sun manta da Musa dake cikin rijiya ma.

Shi kuwa Musa yana dubawa bai ga Lantai ba sai wata ƙaramar Kaza da ko ci bata isa ba sai yayi tunanin ko Lantai tayi ƙasa ne data sha ruwa, ga shi bai iya ruwa ba, amma sai yayi shahada ya nutse ƙasan rijiyar yana lalube ko zai sameta.

Amma sai ya ji kamar ana kiran sunansa daga wajen rijiyar da ƙarfi yana ƙoƙarin yowa sama sai yayi karo da wani dutse a kanshi ya buɗe baki zai ihu ruwa ya cika ma shi baki nan da nan ya nemi nutsewa cikin ruwan don ya fara fita hayyacinshi.

 

Inna Kande ta dubi jikin Lantai ta ce, "Allah Ya tsaremin ke ashe baki faɗa ba amma me ya same ki kike mun wannan uban kira Lantai ?

 

Lantai ta gimtse dariyar dake cinta ta ce, "Yo Inna Kande kazarki ce ta faɗa cikin rijiyar fa shi ne nake kiranki ki zo ki gani ."

 

Sai mutane suka dinga tsaki suna jinjina yarintar Lantai da yadda Inna Kanden ta biye mata duk ta ruɗe.

 

Sai lokacin aka fara ƙoƙarin kiran sunan Musa amma shiru bai amsa ba.

Sai kuma hankali ya tashi aka fara ƙoƙarin neman wanda zai shiga ya fito da Musa.

Lantai ta dubi Kaka ta ce, "Ga shi rijiyar nan Kaka mai rasuwa ya tabbatar da duk randa wani abu mai rai ya faɗa cikinta sai ta ci mutum uku ko ? Inna Kande ta dubi Lantai zatai magana Lantai ta cigaba da cewa, "Ba har yana ce maki akwai ƴan ruwa ba cikin rijiyar ba sune suke sa ruwan rijiyar nan bai ƙafewa duk rintsi ba ko da sauran rijiyoyin ƙauyen nan sun ƙafe ita bata ƙafewa ko ?

 

Sai aka fara kallon kallo mutanen wajen domin dai da gaske rijiyar bata taɓa ƙafewa ba, sannan ba a taɓa yasar taba tunda take .

Ke nan yanzu ta ci Musa da kaza saura wani mutum guda kenan ?

 

Sai mutane suka fara neman tserewa daga gidan.

 

Yayan Musa da shi yaje nemo kwaranga ya shigo kenan ya saka cikin rijiyar ya ji Lantai na cewa,

 

"Wai Inna Kande kin manta sanda yake cewa rijiyar nan ba haka kawai take ba nan ne mahutar Sarkin aljanun ruwa ne ?

 

Ya saki kwarangar ya nufi Lantai yana haki yace, "To dan Ubanki yanzu me kike nufi  kenan wani ya shiga a samu cikon na uku kenan ?

 

Lantai ta fashe da kuka ta ce, " Audu daga faɗar gaskiya sai zagin marigayi Babana ? To daɗin abin ma yanzu kuma za a dinga kiran akwai marigayi a naku gidan.

 

Mahaifin Musa ganin ba mai niyyar shiga don maganar Lantai ta razana kowa yayi ƙundunbala ya shige cikin rijiyar.

 

Lantai kuwa ta sunkuya ta dinga cewa, "Yawwa Babansu Musa don Allah ka ciro kazar  don itama ai mata muhalli."

 

Haushi yasa Inna Kande ta rufe Lantai da duka, su kuwa mutanen gun gudun masifarta yasa basu tasar ma Lantai ɗin ba tunda farko.

Don haka babu wanda ya bata haƙuri ko yace ta bar dukanta.

 

Sai ga mahaifin Musa saɓe da shi yana niyyar fitowa mutane aka kama aka fito da su.

 

Aka kwantar da Musa ana danna cikinsa ruwa na fita bai jima ba ya farfaɗo .

Sai hamdala jama'a ke yi suka ciccibi Musa suka nufi gidansu da shi ko kallon inda Inna Kande ke sukan Lantai basu yi ba.

 

Ranar Lantai yini tayi kuka tana ƙarawa Inna Kande tayi banza ta ƙyaleta ko kallon inda take batayi .

Lantai ta yini kukanta ta gaji ta daina ta ɗauki abincinta tana ci tana hawaye.

 

Tana gamawa ta fice bata tsaya ko ina ba sai gidansu Musa, Innar shi na ganinta ta haɗe rai tayi kicin-kicin da fuska ta kama aikin gabanta kamar bata ga Lantai ba.

Ita kam Lantai ko a jikinta sai ta kama leƙen ɗakunan gidan don taga inda Musa yake kwance.

 

Sai lamarin yarinyar ya daina ba Innar Musa haushi sai mamaki yarinya bata san tai laifi a ɗaure mata fuska ba ko ai mata kora da hali ba ?

 

Lantai kuwa na dube-dubenta ta ci karo da ɗakin da Musa yake, yana zaune yana cin fanke ta kuwa afka da gudu ta ɗauki fanke guda ta cusa a bakinta ta kama ci tana cewa, "Yo ai da  ganinka na zo in maka sannu amma yanzu na rantse na fasa domin yanzu ni godiya ya kamata kai min ma ai."

 

Kallonta yake, yasan abin da ya fi hakama Lantai na iya yi don ba tasan komi ba sai wauta da shirme.

Innasu Musa dake tsaye bakin ƙofar ɗakin ta yi murmushi tana jinjina halin Lantai.

Lantai ta sake ɗaukar wani fanken ta ce, "Yo kai Musa ai gaba ta kai ka domin nasan ka kwana biyu baka ci wannan garar ba, fanke ba ranar kasuwa ba ai sa a ne samunsa sai gidan ƴan gayu."

 

Shi kam Musa sai ya daina cin fanken ya zuba mata ido kawai yana kallonta, ta dubi Innarshi ta ce, "Inna Allah Ya sa dai kin ci naki rabon don ina ji rannan Sale (Ƙaramin yaron gidan) yana kukan yace a sawo ma shi fanke ranar kasuwa ba a sawo ba."

 

Innarsu Musa ta juya tana dariya, ta lura yarinyar ba ita kaɗai bace abin nata yayi yawa.

 

Ta cinye fanken tas ta ɗauki  guda ɗaya ta dubi Musa ta ce, "wannan zan je na nunawa Inna Kande ne nasan zata ji haushi tunda itama ta kwana biyu bata ci ba."

Ta fice da gudunta ba ko sannu ta bar gidan.

 

Tana zuwa gidan ta iske Inna Kande na zaune ta kunna rediyonta tana saurare amma kaɗan-kaɗan ta sauke ajiyar zuciya ta kukan da tasha ɗazun.

 

Sai da ta natsu sannan ta ɗauko littafinta INA HUJJAR TAKE da zummar fara karantawa.

Dafe kirjinta tayi ta zaro ido waje ta ce, "Ina littafin yake ?

 

Ta duba ko ina bata ganshi ba.

Ta fito ta je banɗaki nan ma bata ganshi ba.

 

Ta koma ɗaki ta ci ɗamara ta ce cikin muryar kuka, "Nasha ruwan bala'i yau akwai tashin hankali a ƙauyen nan idan ban ga wannan littafin ba, domin akan littafin nan ina iya tada hankalin kaf mutanen ƙauyen nan."

 

 

To fa ya kenan za ai ?

Waye ya tsinci littafin ?

 

 

Haupha