HAƊIN ALLAH: Labarin Soyayya Da Cin Amana Mafi Muni, Fita Ashirin

HAƊIN ALLAH: Labarin Soyayya Da Cin Amana Mafi Muni, Fita Ashirin
HAƊIN ALLAH
 
   Labari da rubutawa
       
   *Hauwa'u Salisu (Haupha)* 
 
 
 
 
 
 
          Page 20
 
 
 
Kasa rufe bakinsa ya yi, na tashi tsam na bar gun, har na tafi na dawo na amshi naman dake hannunsa na ɗauki leda fara na kwashe mafi yawan naman dan saida ta cika dam, sannan na ƙulle na ba shi nace "Ga wannan ka kaima Safiya tana da rabo a wannan amma a nawa ko tayi tsafi da baƙar Jaba ba zata ci shi ba. Ga wani saƙo mai daɗin faɗa ma zuwa gareta , ka gaya mata duk ranar da ta sake zuwa gidana sai na yi mata abin da yafi wanda nayi mata kwanaki, idan kuma tana ganin ƙarya ne to don Allah ina jiran zuwanta gidana ta sha mamaki." 
 
Duk da a raina ina jin tamkar zai rufe Ni da duka ne jin furucina amma sai naga ya ɗauki naman ya saka aljihu yana cewa, "Masifaffar banza kawai ke dai kika sani kuma ai nan gidan za ki aje komai." Ya sa kai ya fice. Kawai sai naga ai bai kamata ba ma ace shike da wannan Uban naman don haka na ɗauki sauran na haɗe da nawa na rufe na kama harkar gabana ina jin zuciyata na tafasa kamar zata fito waje don baƙin ciki.
 
Bayan sati guda da suna na shirya tunda safe na shiga gun Abban Haidar nace "Zan je gidanmu na kaiwa Mama yaran ta gani Yau, amma zan dawo kafin sanwar ruwan zafi don nayi wankan yamma kan lokaci."
Ya juyo ya kalleni sosai yace, "Wai da gaske wannan karon ba za ki ban komai ba na haihuwar? Ance min ana bada kuɗin karin angon jego fa amma naga ke baki da niyyar bani." 
Da ɗan murmushi na dube shi nace, "Tabbas ana ba da kuɗin karin angon jego daga dubu ashirin zuwa sama amma fa ga angon jegon da ya tabuka abin kirki ya yi bajintar siyen kayan barka ga maijego to tilas a ba shi kuɗin karin angon jego don ya rage hidimar suna dake tafe kanshi. Amma kai nawa ka kashe min tun da na haihu? Me ka siya ka kawo min kace ga shi na barka ne? Ba Ni ba ko yaranka da suka zama dole kai ma sutura bakai masu ba, to nikam me zai sa na kwashi kuɗi na baka don ina tsoronka buge Ni ne ko kar ka kashe Ni?" 
Girgiza kanshi kawai ya yi ya maida kanshi ya kwanta, Ni kuma na fice ina jiran yarinyar Maman Khairat ta zo ta goyanin Afnan na goya Afnah mu tafi.
 
Sai da na tabbatar dana ɓoye nama na sosai sannan na tafi na bar shi kwance.
 
Ina zuwa na iske Mama ba don kar taga hawayena ba tabbas da na fashe da kuka amma ya zan yi? Haka Allah Ya ƙaddara mana Ni da mahaifiyata zamu yi rayuwa irinta ƙunci da takaicin ɗa namiji. 
 
Tabbas ko dan mahaifiyata sai na jajirce kamar yadda Hajjo ta gayamin, dole na zama ɗiya ɗaya tamkar da dubu gun mahaifiyata, dole ne na sakata cikin farin ciki kamar yadda take ƙoƙarin sakani duk da bata da halin.
 
Bayan mun gaisa na kawo dubu biyar cikin dubu goman da Hajjo ta ban na bata da atamfa guda huɗu masu kyau nace ga rarar jikokin nan Mama.
Tai ta godiya , na gyara zama nace "Hajjo tace zan fara saro kaya daga Kano to sai naga ya kamata ke ma ki fara naki sana'ar Mama saboda zaman haka bai da daɗi sam. Ina ga zan baki dubu talatin cikin kuɗin sai ki samu sana'ar da kikasan tana da riba kuma bata lalacewa ki kama, kamar irin ta saida robobi nasan za ki yi ciniki sosai Mama." 
 
Ta dube ni ta yi jim kaɗan sai kuma tace, "Kina ganin hakan ba komai ƴar nan? Da kin barni haka ke kin kama sana'ar sai yafi, tunda kin ga yanzu ba kowa gabana Ni."
 
Na zumɓura bakina nace, "Ai hakan ma kawai za ai, ke dai ki taya Ni da addu'ar Allah Ya shige mana gaba kan lamarin dai kawai."
 
Haka muka Yuni Ni da yarana, gun mahaifiyata cike da ƙaunar juna, motsi kaɗan tace me nake so, ko me zata ban. Ganin angama sallar la'asar yasa na shirya tsab na ɗebo abin da nake buƙata na abinci na tafi gidana ina jin tausayin mahaifiyata fiye da yadda nake tausayin kaina.
 
Ina zuwa na hango gidan a rufe, don haka na leƙa gidan Binta naji ko ya kai mata makullin gidan kafin ya tafi, tace min bai kawo ba. Asalima bai jima da fita daga cikin gidan ba.
 
Na fahimci don nace mai yanzu zan dawo shi yasa ya rufe gidan, ga shi naga alamar tsohuwar dake dafa mana ruwan wanka ta ɗora sanwar. Don haka na fiddo wayata na kira shi, amma kira kusan biyar ba wanda ya ɗauka sai kawai naji har na fusata ban sake bi takan wayar ba na samu ƙaton dutse nasa na ɓalle makullin gidan na shige daman nasan ƙofar ɗakin buɗe take don ba makullin rufe ta sai dai a sakaya kawai. Ina zama tsohuwar na zuwa ta cigaba da iza wutar ruwan wankan har ta tafasa, ta kwashe min na barta tana yi ma su Afnan, tana da kirki sosai matar domin duk sanda ta gama yi masu wanka sai ta wanke min kayansu ta wanke har da na Haidar, hakan yasa nima nake yawan yi mata kyauta iyakar ƙarfina.
 
Ba Deeni bane ya dawo gidan sai bayan magrib irin gab sallar ishsha'i sannan ya dawo. Da yake ƙofar ɗakina na aje kwaɗon don ma ba sai ya sha wahalar nemansa ko tambaya ba. Ina jinsa yana cewa "Wane isasshen ne ya lalata min kwaɗon gida? Ai ko Allah sai kin biyani kuɗin ƙwaɗon nan inga ta ƙaryar rashin mutunci." 
 
Har tuntubar nake wajen fitowa ƙofar ɗakin nace, "Magana kake ne?" Ni ma zuwa yanzu na fahimci yadda nake bala'in haɗe fuska duk idan zan mai magana sai naji tamkar zan kashe kaina don mugun haushinsa da nake ji.
 
Ko ganin irin muguwar hararar da nake watsa ma shi ce tasa ya shige ɗaki yana jan tsaki. Nima ban san ya akai ba na ja nawa uban tsakin wanda ya fi nashi ƙara da sauti.
 
Har ya shige ya sake fitowa, 'Ke wai Ni kike yi wa tsakin?" Fuskata ba alamar tsoro nace, "Kai da kake min kanwa na kasa ne da ba zan rama ba?"   Na wuce shi fuuu na faɗa kan kujera na zauna ina cika ina batsewa.
 
Tunda Deeni ya fahimci ban cikin matsalar komai Ni da yarana kullum sai nayi girki haka mutane na yawan shigowa muna gaisawa ana fira sai na samu kaina da rashin damuwa da lamarin Deeni kwata-kwata bai gabana. Abinci duk lokacin da na dafa ina zuba mai yawan gaske tunda yanzu a cikin mazan unguwa yake zuwa cin abinci.
 
Duk da ina jin shi wani lokacin idan ban gama da wuri ba idan ya aiko nace yanzu zan kawo yai ta masifa har sai sun dinga ba shi haƙuri kamar irin shi ne ya siyo ya kawo min na kasa girkawa da wuri. Ni dai ko tankawa ban yi idan nice na kai abincin yake yin faɗan gabana. 
 
Muna a haka na shirya tsab na nufi Kano don saro kayan da zan cigaba da saidawa. Zuwa yanzu daman Deeni babu ruwanshi da Ni ko harkata balle ta yarana, sai ya ga dama yake ɗaukar su ko da yake yana yawan ɗaukar Afnan don ita ce mai sunan budurwarsa in ji shi nasan duk dan in ji haushi ne amma ko a jikina , kuma shi kaɗai ke kiran yaran da sunansu amma kowa Afnan da Afnah yake kiransu.
 
Har na fice ya kira Ni ta waya, wai na samu yaro na aika mai da ko dubu guda ce bai da kuɗi. Kamar ince babu sai kuma na ce to, na aiki yaron Binta nace ya kai mai.
 
 
                    KANO 
 
 
Tun a mota na kira Uncle Salim na gaya mai ina hanyar zuwa Kano.
Ina sauka tashar mota na iske Uncle Salim na jirana, don haka ban sha wahala ba muka isa gidan Hajjo.
Hajjo na gani na ta rumgume ne tana ta jin daɗin yadda ta ganni babu muguwar  kama kamar lokacin da nake goyon  Haidar. Abinci mai rai da lafiya na iske an aje min, na ci iyakar ci na, mu kai ta labari da Hajjo da Uncle Salim. Uncle Salim ya miƙe tsaye ya ce, "Jiddah bari na fita Mustapha na jira na waje za mu je wani waje sai na dawo."  Ni da Hajjo muka bi shi da adawo lafiya.
 
Hajjo ta dube ni "Ya kamata ki shiga wajen ƙawarki Zainab ko da yaushe tana yawan maganarki idan ta shigo gidan nan." (Zainab ƙawata ce nan makwabta tun zamanin zama na gun Hajjo tamu ta zo ɗaya da ita) na miƙe na ɗauki Afnan sai kuma naga barci take don haka na aje ta na wuce ina ce ma Hajjo sai na dawo.
 
Kamar walƙiya haka yaga wulƙinta ta wuce idan ba gizo idansa ke ma shi ba gidanshi ta shige. Shi kam yarinyar na birge shi sosai yake jin tana ba shi sha'awa tana da kyau haka tana da jiki mai kyau da tsayawa a zuciya. Tun shekarun baya ya so nuna mata so sai ya wayi gari bai san yadda tai ba, ya yi nauyin bakin tambayar abokinsa Salim labarin yarinyar har ta kai lokacin da Salim ke gaya mai ta yi aure, hakan yasa ya cire ta daga ranshi amma yanzu yana ganinta sai da ya ji ina ma ace matarsa ce?"  Ko da yake shi yanzu ba ta mata yake ba domin ya yi masu kuɗin goro duk kanwar jace basu da amana  haka basu da kirki sam basu san darajar na tare da su, amma yana ji a jikinsa duk da tabon da mata su kai masa a zuciya idan zai masu waccan yarinyar tabbas zai murna ba mamaki babban burinsa ya cika sanadin ta.
 
Haka Mustapha yai ta saƙawa da kwancewa kan Jiddah wadda ita sam bata ma san yana yi ba duk da cewar a zamanin zamanta gun Hajjo ta san shi amma ba irin sanin nan ba na sosai da sosai ba, amma tabbas idan ta ganshi zata shaida shi ganin farko ma kuwa.
 
Uncle Salim ya dubi abokinsa da fuskar tausayi yace, "Bai kamata ba ace ko da yaushe kana aje abu cikin ranka ba, saboda bai da wani amfani ka sani Allah shi kaɗai ne zai iya magance maka damuwarka, wallahi watarana sai kaga kamar ba a yi ba." Mustapha ya dubi abokinsa ya ja numfashi kawai bai ce komai ba, domin ya manta da wata damuwa da yake cikinta ma sam ganin waccan yarinyar da tunanin abin da ya faɗo mai. Da haka suka tashi suka wuce kowa na tunani a ransa, shi Mustapha yana jin tamkar ya tambayi Salim me ya kawo Jiddah amma yana jin kunya sosai. Shi kuma Salim yana tunanin wace irin sana'a ce ta dace da Jiddah matsayinta Na mace kuma yarinya ƙarama? 
 
Jiddah kuwa tana shiga gun Zainab suka baje suna ta fira har akai sallah bata koma gidan Hajjo ba, sai ga Hajjo da Afnah ta kawo tana kuka, aikuwa sai faɗa take masu su duka sun banzatar da yara suna ta firar banza da wofi. 
Zainab ce tana dariya tace, "Kin ga Hajjo gidan su Maryam fa ta iske ni ko can ma mun jima kana muka dawo nan kin ga ai bata jima nan gidan ba sosai kenan?" 
Ita dai Hajjo tai banza da ita ta wuce tana cewa bari na kawo gudar ita tafi haƙuri don barci take ma.
 
Zainab ta amshi Afnah tana ta murna, "Oh ikon Allah! Yanzu Jiddah ke ce da yara har uku?"  Ni da ita muka kwashe da dariya, Hajjo ta shigo ta kawo Afnan Haidar na bin ta a baya, amma sai ya ƙi tsayawa ya bita suka koma tare.
Sai da mijin Zainab ya dawo sannan na koma gidan Hajjo.
Akan hanyar ne naga Mustapha na ɗan tsaya in gaida shi naga kamar bai gane Ni ba, don haka na wuce abuna na faɗa gida.
 
Sai da na kwana uku sannan muka shiga kasuwa da Hajjo ta kaini gun ƴan takalma da gun ƴan atamfofi da shadda har da leshi , da ita su kai cinikin komai aka gama aka rubuta komai a takarda da farashinsa, mu ka dawo gida.
 
A gida ne aka fitar mun da kuɗin kowane kaya yadda zan sai da shi, na shiga gidan Zainab don yi mata bankwana tun da gobe da wuri zan tafi gida.
 
Yana zaune yana jin cewa duk duniya shi ne kawai ke da irin wannan ƙaddarar ko kuwa shi ne bai dace ba? Me yasa ya kasa dacewa ne shi? Me yasa duk yadda ya so ya rayu cikin farin ciki hakan ke faskaruwa? Ina ma ace bai yi aure ba? Kawai ya ganta ta shige makwabtanshi fuskarta ɗauke da murmushi kamar ko da yaushe, tsab da ita ga alama bata da wata damuwa don duk lokacin da zai ganta a cikin farin ciki take. "Allah ka kai damo ga harawa." Ita ce kalmar da zuciyarsa ta ayyana mai bai san ya akai ba kawai ya ji ya saki murmushi mai tafe da sauti ba.
Bata jima ta fito yana ganin matar gidan ta rako ta ga alama bankwana suke. Sai ya ji take tamkar ya yi mata magana su gaisa amma daya tuna da tana da aure sai ya fasa kawai ya juyar da kansa gefe kamar bai ganta ba.
 
Har ta zo ta wuce ta gabansa yana kallonta ita kam ko inda yake bata kalla ba, ta shige gidansu Salim. Ajiyar zuciya ya saki kawai ya ji sabuwar damuwa ta dabaibaye shi baki ɗaya.
 
Washegari da sassafe Uncle Salim ya kaini tasha ya biya min kuɗin mota da kuɗin kayana ya ƙara min da wasu kuɗin, sai da ya ga tashin motarmu sannan ya bar gun.
 
Kasancewar na fito da wuri sai na iso da wuri, nan da nan na bugama waɗanda na gayama wa zan je sarin kaya, kafin kace me ? Gidana ya cika da mutane masu duba kaya, kowa ya zaɓa ina rubuta sunan mutum da abin da ya siya da kuɗin sai ƙarshen wata ya ban kuɗina.
 
Cikin ikon Allah kayan basu jima ba na saida su, duk da cewar na fahimci babu wasu kayan tunda a rubuce aka ban sai ban damu ba, na ɗauka mutanen dake zuwa siya ne ake samun marassa tsoron Allah na ɗauka, ashe ba haka bane ba, duk lokacin dana fita zuwa gidan biki ko suna ashe sai Deeni ya kawo mace gidan idan sun gama abin da za su yi sai ya bata takalmi ko atamfa ko leshi, abokansa kuwa yai masu tallar shadda suka ce ya kai, ya ɗibi guda huɗu ya kai ban da labari. 
 
Ranar wata Alhamis ina zaune ina ta ƙoƙarin lallashin Afnah tana ta kuka wata yarinya ƴar ƙauye mai tallar fura ta shigo gidan. Na kalle ta naga ban santa ba kuma ban kira ta ba don haka nace mata lafiya? Shi ne ta ce min, "Don Allah maigidan na nan?" Nace mata "Bai nan amma lafiya kike nemansa?" Sai ta sauke ƙwaryar furar ta fiddo leda baƙa ta ban, tana cewa, "Daman wannan takalman zai sauya min sun yi min yawa in ji Innata." Na amshi takalma da fuskar mamaki ina kwance leda naga takalman saidawa ta ƴan dubu biyu da ɗari biyar, na dube ta nace, "Ke ya akai waɗannan suka zo hannunka?"  Kanta tsaye tace min, "Rannan ne mu ka zo Ni da budurwarsa Hinde suka ce na jira su suka shige ɗaki to bayan sun fito ne na ganta da takalmi da atamfa shi ne nace ina so ya ce na bada Naira dubu na zaɓa na shi ne, to na ba shi dubun kuma naje gida na gwada ance bai min daidai ba na zo ya sauya min wasu ko da irin na Hinde ne."   Yanzu na gano bakin zaren, kenan dai da hajata Deeni ke bin matansa da kuɗaɗe na yake sallamar karuwansa?  Na ɗauki takalmi na kai ɗaki na aje na fito nace mata, "Ki tafi cikin gari ki neme shi ya baki wasu takalman amma ki gaya mai matarsa ta ƙwace waɗannan ruwansa ne ya baki wasu ko ya biya ki kuɗinki. Sai taimako na gaba da za ki min, na miƙa mata naira ɗari biyu nace, "Gobe idan kun fito talla da waccan yarinyar ki zo mun nan gidan da ita don Allah kin ji?" Idan kika kawo ta ki dawo washegari zan cika maki ɗari uku kin ga ɗari biyar ta tashi kenan.
 
Da murnarta kuwa ta fice nayi mata kwatancen inda zata iske Deeni na samu waje na zauna sai kuma na tashi na ɗauko list ɗin kayan da na zo da su dana wanda na saida na fara lissafawa ina ƙoƙarin gano abubuwan da babu a ciki.  Ba ƙaramin mamaki nayi ba lokacin da na fahimci Deeni ya kwasar min kaya masu yawan gaske, nan da nan kaina ya fara juyawa na rasa me ke mun daɗi sai kawai na goya Afnah na saɓa Afnan na nufi gidansu Maman Khairat daman Haidar na can.
 
Allah kaɗai ya kaini gidan lafiya na zube ban sake sanin inda kaina yake ba, sai bayan dogon lokaci na dawo hayyacina. Mamar Khairat ta tambayeni abin da akai min da zafi haka na kwashe na gaya mata. Jinjina kanta kawai tai ta kasa cewa komai. 
 
Sai dare sannan na koma gidan nasan ko kwana zan ba zai damu ba haka idan na koma ba zai ce ina naje ba, yanzu rayuwa muke gidan tamkar kowa zaman kansa yake sai mu yi sati bai tanka min ba sam. Ni ma yanzu na ƙware sosai da nuna halin ko'in kula da rashin maganar don haka ban damuwa sam.
 
Har ya dawo gidan ya kwanta, kamar na je ɗakin nashi mu yi ta cikin daren sai kuma nace bari sai gobe idan yarinyar ta zo sannan sai ayi ta baki ɗaya idan ya so  gidan ya ƙone baki ɗaya.
 
Washegari kuwa har wajen ƙarfe ɗaya na rana ba yarinya ba labarinta balle naga ƙawarta da aka ba kayana, har na fitar da rai sai naji ance " Za ku sai fura?" Har ina taune harshe gun cewa " E za a siya kawo."  Sai kuwa ga yarinyar jiya da wata tare da ita, da fuska ta nuna min ita ce yarinyar, aikuwa na ce su sauke na dubi ƙofar ɗakina naga kwaɗon na nan ma dubi yarinyar nace " Don Allah shiga daga can cikin ɗakin ki ɗauko min wurin da zan zuba furar." Ta kuwa shige na kuwa bi ta da sauri na ja ɗakina na datse na ɗauki cikon kuɗin yarinyar jiya na bata, nace maza ki je gidansu ki ce matar wanda ya bata kaya da suka gama iskanci rannan ta rufe ta a ɗaki tace sai an biya ta kuɗin kayanta zata buɗe ta." 
Har ta tafi nace ki fara biyawa gun abokin iskancin nata ki gaya mai na datse karuwarsa a ɗaki nace sai an biyani kuɗin kayana."
 
Na koma na samu waje na zauna sai kuma naga gwara na kai yarana ajiya kada ma su hanani rawar gaban hantsi idan Deeni ko iyayen yarinyar sun zo.
 
Na kuwa miƙawa Binta su nace ta riƙe min su zan shiga wanka amma sai na fara gama wanke kayansu.
 
Ban jima da dawowa ba sai ga Deeni, zuwa lokacin yarinyar sai uban ihun kuka take cikin ɗaki nikam ƙala bance mata ba, domin ban tsara zance matan ba sai gaban iyayenta ko wanda ya bata kayan nawa.
 
"Ke lafiya za ki rufe masu yarinya a ɗaki?" Na dube shi naji kamar na kife shi da mari nace, "Lafiyar ce ta saka haka, amma idan ba a biyani kuɗin kayana da aka bata ba wallahi tallahi sai dai ta mutu cikin ɗakin can." 
 
Har ya zaburo da gaske zai kama Ni da komowa nace, "Dakata abin bai kai nan ba da farko amma tunda ya kai yanzu shege ka fasa to." Na gyara tsayuwata na dunƙule hannu ina jiransa.
 
Ban san yadda akai ba naga ya ja baya ya ce, "Don Allah ki buɗe mata ƙofa sai mu yi maganar daga baya kar kisa ta tara min mutane a banza." 
 
Na waro idanu waje nace, "Kasan Allah ba mutane ba ko aljanu ne za su zo nan gidan Yau sai an kawo min kayana ban san kuɗin ma kayana nake so wallahi." 
 
Tun muna yi kaɗan har abu ya kai makwabta sun fara jiyo kukan yarinya da tashin muryarmu sama-sama don haka mutane suka zagayo jin abin da ke faruwa. 
 
Muna cikin hakan iyayen yarinyar suka zo sai kuma aka ci sa'a ashe yarinyar ba gidansu ta kai kayan ba gidan ƙawarta dake da aure takai kayan domin itama an kusa bikinta nan da sati biyu don haka tana gudun ta kai su gidansu ace ina ta samo su, don haka ta kai ajiyarsu.
 
Akai-akai da Ni kan na buɗe ɗaki yarinya ta fito nace sam, ban buɗewa sai na kama kayana a cikin hannuna sannan zan buɗe mata ɗaki.
 
Ubanta ya leƙa ta taga ya tambayeta ina kayan suke? Tana kuka tana gaya masu inda ta kai ajiyar kayan. Uwarta ta saka Salati  tace "Kin banu kau dan Fure ta je garinsu Tani barka sai gobe zata dawo, e wallahi kin ja wa kanki tsiya Hinde."
 
Ganin anyi juyin duniyar nan na kafe ban buɗe ɗakin yasa iyayenta da Deeni suka haɗa kuɗaɗen dake aljihunsu suka ban suka ce na buɗe ta gobe idan an kawo min kayan sai na basu kuɗin tunda sun fi na kayana ai kuɗin.
 
Na ƙirga naga dubu huɗu ce daga Deeni sai dubi shida daga Innarta dubu takwas daga Babanta na soke a zanina nace "Na rantse da Allah idan ba a kawo min kayana ba sai na ba su mamaki." 
 
Sannan na buɗe ta, tun kafin ta ida fitowa ubanta ya kai mata duka uwar ma ta kawo nata, naga suna neman sabauta yarinya cikin gidana na janye ta bayan na tabbatar da ta bugu sosai nace, "Ba dai nan gidan ba, su bari har su je can gidansu sai su yi mata koma miye." 
Suka kwasa suka fice yara na biye da su Ɗuuuu duk ƴan tallar ne ba mamaki ƴan ƙauyensu ne ma.
 
Ko da kowa ya watse na zabura zan miƙe tsaye kawai sai naga Deeni ya kwasa da gudun masifa ya bar gidan har yana yada wayarshi.
 
To masu karatu ko ina Deeni zai je kuma? 
Waye Mustapha me ke damunsa?
Wane irin zama Jiddah ke yi yanzu a gidanta? 
Shin zata kuwa bada kuɗin bayan an kawo mata kayan?
Dama wasu abubuwan duk za ku ji su a page na gaba.
 
Taku a kullum Haupha!!!