HAƊIN ALLAH:Labarin Cin Amana Mafi Muni, Fita Ta Huɗu

HAƊIN ALLAH:Labarin Cin Amana Mafi Muni, Fita Ta Huɗu

HAƊIN ALLAH

   Labari da rubutawa
       
   *Hauwa'u Salisu (Haupha)* 



    Page 4


*Wannan shafin na sadaukar da shi ga Prince ɗina, ina ma shi addu'ar Allah Ya ci-gaba da buɗe ma shi dukkan wasu ƙofofin nasara Ya ƙara ma shi basira da ɗaukaka tare da kare shi daga dukkan maƙiya na gida dana waje Ya azurta shi da dukkan cikar burinsa.* 

Sai da mahaifina ya shafe wata takwas bai dawo ba abin da ya fusata iyayen mahaifiyata kenan, ƙarshe har ta haifi abin da ke cikin bai dawo ba, wanda ta samu namiji aka saka ma shi suna Muhammadu sai bayan ta yi arba'in ne mahaifina ya dawo da iyayen magungunan gargajiya kala-kala. Bayan ya huta ne Kakata ke gaya mai abin da ke faruwa, ya ce "Wallahi ina son matata don haka bari na je na dawo da ita." Ko kallonshi bata sake yi ba, domin tasan iyayenta da ita kanta matar ba wanda zai amince da buƙatarsa. 
Yamma nayi ya yi wanka ya kwashi yaransa suka nufi gidan surukansa, sai dai tun kafin ya shiga mahaifinta yace "Yawwa fatan takardar ce ka kawo min ? Ai ba sai ka shiga ba, ni kaina idan ka bani ya wadatas yaronka kuma idan ka so ka bar mata idan ka so ka ɗauka ka haɗa da ƴar'uwarsa duk ya rage naka."   Da gaske yake yana son matarsa bai shirya rabuwa da ita ba, don haka ya yi ta bada haƙuri amma kamar yana ƙara zuga tsohon dole ya tafi ba tare da yaga ko da kalar yaron da aka haifa ma shi ba balle fuskar matarsa.
Abu kamar wasa ƙaramar magana ta zama babba, ba irin magiya da mutanen da bai tura ba amma ita da iyayenta suka kafe kan bata komawa sam, daga ƙarshe sai tace ma shi ita fa ban da yawon da yake hatta tabar da yake sha ƙona mata zuciya take don haka kawai su rabu ta gaji da halayensa ita. Daga ƙarshe dai yana ji yana gani ya rubuta mata takardar sakinta ya bata. A lokacin yarinyarsu nada shekara uku da rabi don haka bai shawara da kowa ba ya ɗauke ta ya kaita Lagos gun wata Inyamura Iyami mai saida abinci yace ta rike ma shi yarinyarsa ya bata amana domin duk sadda ya kalli fuskar yarinyar sai yaga ta mahaifiyarta, har zuwa yanzu bai daina jin son matarsa a ransa ba, duk ya takura kansa ya daina zuwa daji ya daina shan taba amma ta yi mirsisi tace bata dawowa don haka ne ma bai san ganin fuskar yarinyar na tuna mai da mahaifiyarta.

Kun san dai yadda yare suke da son banza ko da Iyami  taga yadda yake matuƙar kula da yarinyar ko da yaushe cikin kashe manyan kuɗaɗe yake sai tai na'am da yarinyar ta dinga nuna mata soyayyar ƙarya a gabansa, ko da wasa bata barin yarinyar tai kuka, duk abin da take hankalinta na kan yarinyar, abin da ya ƙara mata kima da yarda ga Baban yarinyar, ya kimtsa ya aje mata manyan kuɗaɗe yace zai tafi sai bayan shekara zai dawo amma zai dinga yi masu aike na duk abin da suke buƙata.
Haka Babana ya tsallake ni ya barni gun wadda bai da haɗin komai da ita, asalima ba musulma bace ba. Tunda ta tabbatar da Babana ya bar garin shike nan sai ta ɗauki tsanar duniya ta ɗora min, sam bata tausayin ƙaranta ta, wahal da ni take tamkar wata yarinyar budurwa, duka da zagi kuwa da suna kanta da sun yi min a jiki. Duk wanda ya sai abinci nice ke kai ma shi duk kuwa inda yake, tun ban iya wanke-wanke ba har dai na iya da duka da zagi, duk da cewar abinci take saidawa amma bata bani wanda zan ci in ƙoshi, sai dai ta ban wanda zan lasa, hakan yasa nake ta tsawo ba ƙiba, duk na fice hayyacina a shekaruna bai kamata ace ina wasu ayyukan ba amma duk na jima da ƙwarewa da iya su, hatta wankin kayanta don mugunta nice ke yi mata su, kayana kuwa ta tattara ta ɓoye su kala biyu kawai taban nake sawa sai kaya sun sati biyu jikina take cewa na cire na wanke na saka gudan kayan. Akwai yaran Babana da dama dake gun suna ganin halin da nake ciki amma basu isa su tanka ba, domin muguwar masifaffa ce Iyami sam bata da mutunci ga shi tari ga ta yaudare shi ta nuna ma yarinyar ƙauna a gabansa ta ƙarshe don haka ba abin da za a gaya mai kanta ya amince. 

Shekaru na ta tafiya har na kai shekara shida a gun Iyami, zuwa yanzu ita kanta wahala idan ta ganni sara mun zatai, domin yanzu hatta girkin da take yawanci duk nice jigonsa tana daga zaune take sakani komai iyakarta ta kame kan kujera tana bani umarni ina bi. Duk da ƙarancin shekaruna hakan bai hanani gane irin wautar da mahaifina su kai ba na kawoni gun wadda ba musulma ba, gani kara zube babu arabi babu boko aiki kawai nake kamar inji, bata taɓa ce min nayi sallah ba, to idan tace min ma ban san yadda ake yinta ba ai balle inyi don haka ni da ita babu bambanci sai na suna da shigar kayan jikin mu kawai.
Sule yaron Babana ne shi ne kawai ke jin tausayin halin da nake ciki yana matuƙar tausaya min sosai kan abubuwan da Iyami ke min, ya sha siyen abinci idan na kai ma shi yace na zauna na cinye ya ban kuɗin na kai mata, shi ne yake yawan ce min na dinga sallah na dinga yi ma iyayena addu'a duk sanda nayi sallah. Duk lokacin da yake gaya min hakan kallon shi kawai nake domin ban san yadda ake sallar bama sam da ya fahimci hakan naga alamar tashin hankali muraran kan fuskarsa, an fi sati ya zo shagonmu ya ba Iyami kuɗi masu dama yace "Oga ya aiko da su yace na kawo maki ki saka yarinyar can makarantar boko da arabi to amma ni a shawara ta me zai hana ki damƙe kuɗaɗen ki samu wasu makarantun na ya ku bayi ki cilla ta duk wata ki dinga amshe kuɗin da zai turo kina ƙara jari tunda kuɗin makarantar kuɗi ne ya bada ki saka ta?"    
Murmushin jin daɗi tai tace, "Shegiya Sule ashe kanki na kawo wuta."  A nan take ta ba shi aikin nemo min makarantun talakawa. Idan ba haka ya yi mata ba, ba zata taɓa amincewa yarinyar tai karatu ba, shi kuma yasan hakan shi ne kawai abin da zai ma Ogansa ya rama rabin abin da ya yi ma shi a rayuwa, domin shi ne ya kawo shi Lagos ya sai mai mashin yake haya kuma bai taɓa amsar ko da Naira dubu ba daga hannunsa kyauta ya sai ma shi mashin ɗin, don haka ya ga dacewar yin hakan ga ɗiyar Ogan.

Cikin kwana biyu na fara zuwa makaranta sai aikin wahala ya rage min, sai dai tana yawan hana ni abinci tace, "Can makarantar ba a baka ba ne don ubanka?". Idan da sabo na saba da yunwa da wahalar rayuwa don haka sam ban damuwa da abin da Iyami ke mun tunda na riga na gane ba ita bace ta haifeni ba sai abin ya yi min daɗi domin yanzu na fahimci illar rashin addini.

Alawiyya Malam ita ce kawai ƙawata, wadda muka shaƙu muke tattauna magana kowace iri a tsakaninmu, babu nisa tsakanin gidansu Alawiyya da gidanmu don haka duk sanda zan je makaranta ina fara biya mata sai mu wuce, Kakar Alawiyya Inna Kande tana da matuƙar kirki da tausayi ko da yaushe ita ce ke wanke kayan Alawiyya ita ce ke girka abincin da Alawiyya ke ci ita Alawiyya goro kawai take saidawa, daga shi babu aikin da take ma Inna Kande hakan yasa Alawiyya ta fini kumari ta fini walwala da natsuwa ko da yaushe ni cikin tunani nake ko ya sunan iyayena oho, ko ya kalarsu take oho, naji dai su Sale na kiran mahaifina da Oga Dawa ko hakan ne sunanshi oho, ko a makaranta ni kaɗai ake kira da Jiddah Iyami kowa da sunan Babansa sai nice kawai ban da sunan mahaifi a jikin sunana. 

Tunda mahaifina ya tafi bai sake waiwayar halin da ƴarsa take ciki ba sai zafin aike da tambayar ya Jiddah take aikin kenan bai taɓa cewa bari ya zo yaga ya halin da nake ciki ba ko yace ya kamata yaga ya na koma ba. Rayuwarsa kawai yake bai damu da duk halin da zan kasance ba, shi dai tunda ya ba da ni kuma yana turo ma Iyami da kuɗaɗe shike nan a ganinsa ya gama mai wahalar.

Muna zaune ni da Alawiyya take gayamin Inna Kande tace zata je garinsu don haka zata zo gun Iyami ta nemi alfarmar ta riƙe mata Alawiyya har ta dawo daga ganin gida. Ba ƙaramin daɗi naji ba na maganar domin har ga Allah ina matuƙar jin daɗin zama da Alawiyya domin tana tayani ayyuka da dama, kuma tana yawan kawo min abinci a ɓoye, haka duk inda zan kai abinci tare muke zuwa da tallar goronta bisa kanta. Haka kuwa akai Inna Kande ta zo gun Iyami ta gaya mata zata je gida can Arewa gun danginta amma ba zata je da Alawiyya ba saboda wani babban dalili mai ƙarfi amma don Allah ga ajiyar ta nan zata bar mata kafin ta dawo. Da farko Iyami kamar ba zata amsa ba, sai da Inna Kande ta fito da kuɗaɗe ta miƙa mata tace, "Ga waɗannan ko da zata buƙaci wani abun kafin in dawo Iyami." Nan take Iyami ta washe baki ta amshe kuɗin har tana tambayar "Halan zaka jima ne can?" Kowa yasan mugun son kuɗin Iyami don haka duk wanda zai mata tarko da su yake mata bata ƙara awa guda take faɗawa. Inna Kande ta kiramu ni da Alawiyya tace, "Zan tafi garinmu amma zan gaya maku labarin yadda nake da ke Alawiyya (ta nuna Alawiyya da yatsa) ba don komai ba sai don yanayin rayuwa, ban san abin da gaba za tai ba.
Alawiyya ki sani nice mazaunin Kakarki tabbas amma ba nice Kakarki ba sam! Ba Alawiyya ba hatta ni sai da na kalli Inna Kande, domin duk da ƙarantata nasan lokacin da Innar Alawiyya ke zaune a gidansu kuma Inna take kiran Inna Kande, haka a gabansu tai aure ta auri wani soja suka tafi tare ta bar Alawiyya hannun Inna Kanden.  Amma yau ga shi tana maganar wai ba ita ce Kakar ta ba... Inna Kande ta ci-gaba da cewa, "Mahaifiyarki na santa ne a motar da muka shigo na zuwa nan garin daga Gombe duk cikin motar ita kaɗai ce budurwa domin duk mun manyanta mu tunda da niyyar bara muka fito daga gidajenmu zuwa Lagos tunda mun ji ance ana samun kuɗi da bara a Lagos. Tunda muka shigo motar da yake tafiyar dare ce na lura da yarinyar kuka take sam bata cikin hayyacinta sai ta jima tana kuka sai kuma ta koma tunani, duk inda aka tsaya don a ci abinci ita bata cin komai kuma bata siyen komai, sallah kawai take yi ta koma kurerarta tai ta kuka. Hakan yasa da aka tsaya cin abinci na ga kowa ya fice daga motar ban da ita na je nayi mata magana nace, "Baiwar Allah lafiya kike tafiya cikin ƙuncin rayuwa ne? Shin me yasa ke tunda muka taso baki ci abinci ba kuka kawai kike da tunani?" 
Sai da ta goge hawayenta sannan tace min, "Ni ɗin daga ƙasar Chadi nake sunana Hajiya Fatima iyayena suna da arziƙi dai-dai gwargwado don mu duka ba wanda bai ke aikin hajji ba a gidanmu ni kaɗai ce mace a gidanmu sai Yayyena maza su huɗu, muna rayuwa cikin kwanciyar hankali da wadata kwatsam aka fara rigimar boko haram a garin Chadi hakan yasa muka koma cikin Niger da zama mu duka, sai dai mun yi asarar dukiya mai yawan gaske wadda tasa muka dinga rayuwa a cikin talauci a Niger, a hakan watarana kwatsam mu ka ji mutane nata gudu suna ihun an kawo hari Niger ɗin ma, mu ma muka bi ayarin ƴan gudun hijira mu kabar Niger a jigace, sai dai lokacin da muka isa Nigeria kai tsaye Jigawa muka nufa, Allah da nashi ikon hatsari ya gitta mana a nan ne na rasa halina ban san inda suke ba, don ni dai na tsinci kaina a gadon asibiti ance mun kuma rarraba mutanen cikin motocin da sukai hatsarin akai, na yi iyakar nema na amma ban ga ko da mutum guda ba na ahalina shi ne akai min hanyar zuwa Lagos don zuwa nayi bara na samu abin ci da kaina."  Ko da naji labarin Fatima sai tausayi ya yi masifar kama ni don haka nace ta kwantar da hankalinta idan mun sauka ni zan riƙe ta kar ta saka damuwa a ranta, insha Allah watarana zata haɗu da mutanen gidansu. Tun da muka iso Lagos na kama mana hayar gidan da muke ciki na fara fita bara sai ta hanani tace gwara mu nemi sana'a sai ya fi zuwa barar nan mutunci, na yarda da shawarar ta muka fara sarin biredi da lemu muna saidawa cikin ikon Allah kasuwar ta amshe mu kamar wasa a haka wani saurayi  mai suna Bello yace yana son Fatima ta nuna bata amince ba da farko sai daga baya ta amince da shi domin ni kaina na yaba da halayensa yana sana'ar wankin mota ne a nan Lagos yace shi ɗan asalin Kano ne neman kuɗi ya kawo shi nan Lagos. Cikin mutunci akai aure suka tare gidan hayar daya kama masu zamansu gwanin ban sha'awa, sai da Fatima ta shekara uku bata samu ciki ba sai a ta huɗu ta samu cikinki, ta sha matuƙar wahalar kwaikwan cikinki kamar ba za ta tashi ba har dai aka haife ki, kina da shekara guda dangin Bello suka bayyana basu yi wata-wata ba suka ɗauke shi suka ce basu yarda da auren da ya yi ba don haka ko ƴar basu so, yana kuka yana komai ya saki Fatima saki guda ya ban amanar ki yace duk daren daɗewa zai dawo ya tafi dake. Bayan tafiyar Bello Fatima ta shiga gararin rayuwa na kewa da soyayyar mijinta sosai domin Bello mutum ne har da rabin mutum, ya san yadda ake fita haƙƙin iyali yadda ya kamata. Sai ga wani soja ya bayyana da ƙarfinsa yana son Fatima ita kuma tace ta gama aure zata zauna ta kula da yarinyarta har abin da Allah Ya ƙaddara. Sojan nan yai ta naci yai ta ƙwaƙwa amma Fatima ta kafe kan bakanta hakan yasa hankalin sojan tashi ya dinga yini gidanmu yana mata magiya yana neman na saka baki ta amince ya aureta ƙarshe dai da naga mutane sun fara gulma na saka baki Fatima ta auri sojan nan mai suna Aliyu nan da nan aka saka biki wata guda yace kuma a nan zasu zauna sai bayan bukin da wata shida Fatima ta zo tana kuka take gaya min an sauya mai wajen aiki zuwa Taraba kuma yace da ita zai tafi. Babu yadda muka iya ni da ita dole muna ji muna gani na bar Fatima ta bi mijinta ke kuma aka bar min ke nan. Abin da yasa ba zan je da ke garinmu ba ban so ne ai maki wani kallo wanda bai kamata ba, ba shakka sai nafi kowa kukan mugun sunan da za a dinga jifanki da shi,sannan ina ji a jikina duk inda Babanki yake yana tafe gareki gwara ki zauna a nan kar ya zo baki nan, insha Allah ba zan jima ba zan dawo gareki Alawiyya." 

Ba ƙaramin kuka muka sha ba jin labarin mahaifiyar Alawiyya ba, amma duk da haka sai naji gwara ita tunda ko banza tasan asalinta ni fa? Ban san nawa asalin ba ko sunan iyayena ban sani ba. A ranar Inna Kande ta wuce garinsu ta bar Alawiyya gidanmu gun Iyami.

Cikin sati guda Iyami ta fito da sabon salon azaba da musgunawa garemu wanda ya ninka wanda take min a baya. Ga shi Inna Kande shiru bata dawo ba har ta share wata uku ba ta ba labarinta . 

Watarana muna makaranta Sule ya zo cike da farin ciki yake shaida min ga Babana can ya zo. Ni da Alawiyya muka fice da gudu cike da farin cikin murnar Yau zan saka mahaifina a cikin idanuwana.


Shin da gaske Jiddah zata haɗu da mahaifinta kuwa?

Me yasa Inna Kande bata dawo ba?

Ina labarin mahaifin Alawiyya da mahaifiyarta?

Da su da wasu amsar duk zaku ji su daga taku a kullum Haupha!!!!!