ANA BARIN HALAL..: Fita Ta 19
ANA BARIN HALAL..:
*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE*
*BISMILLAHI RAHMANIR- RAHIM*
*PAGE* 19
Har wayan ta yanke ban ɗauka ba, ƙira na biyu ya sake shigowa shima har ya yanke ban ɗauka ba, daga nan bai sake ƙira ba, kallo na hafsy ta tsaya yi, chan dai ta kasa haƙuri tace, "Adda kaman ƙiranki naga Yayah M.G nayi?" kallon wayan nayi ba tare da nuna mata wani alama da zata fahimci komai ba nace, "kinsan shi da son labari yanzu sai ya hanani abun da nakeyi, ni kuma abunda mamie tayi yau na duk ya ɗaga mun hankali bana jin son magana, shi kuma yanzu zai fara tambayan yyh nake me yake faruwa?" na faɗa ina ɗaukan wayar don na maida ita silent.
"Allah sarki Adda ae mai sonka ne yake damuwa da damuwanka, ni kuma wallahi bakiji yadda nake son ki da yayah M.G ɗin nan ba, don ranan ma sai da mukayi ta gulman ki nida yayah ishaq", ta ƙarasa tana dariya, na ɗago kai ina kallon ta cike da mamakinta, "gulma na kuma name kukayi ke da yayah ishaq ɗin"? Dariya ta cugaba dayi sannan ta dawo kusa dani ta zauna, hannun ta tasaka ta dafa kafaɗa na tana magana cike da dariya a fuskanta, "kina rawa yayah M.G yana miki liƙi kukayi bala'in yin kyau, shine yayah ishaq yake tambaya nah saurayinki ne? Nace mishi a'a kawai kuna shiri ne, sai yace Allah yasa shirin ya koma soyayyah don kun dace da shi sosai, kuma wallahi Adda kun dace sosai ga shi kyakkyawa da shi, don ni yafi mun wancan ɗan'uwan shi mai ɗaurarren fuskan", ta faɗa tana wani ya mutsa fuska.
Nidai murmushi kawai nayi bance mata komai ba, don ko ni M.G yana burgeni kuma kyaun shi yana mun kyau, fara'ar shi tana sakani nishaɗi, da fatan nasu zai zama gaskiya da nayi farin ciki sosai, amma dai iya zuciyata na bar abun.
Washe gari muka lula birnin tarayyah mu da ƴan'uwan mu da matayen su, koda mukaje gidan mai gadi ne ya buɗe mana gate, babu laifi compound ɗin zai iya ɗaukan motoci guda uku, ga flowers masu kyau da ƙamshi a shuke, gidan sama da ƙasa ne, ƙasa shine na Yaya mohd sama kuma yayah Ahmad, da shike kafin biki Aunty B da yayah sun zo sun saka komai a gidan su, amaryah ma anzo an mata mata jeren, kawai ɗan sharewa da gogewa kawai mukayi, sannan aka shimfiɗa bedsheets, a side ɗin yayah mohd muka sauƙa nida fatima da hafsy, su yayah umar kuma hotel aka kama musu, amma munyi hira tare dasu, kuma babu abinda muka girka, order kawai aka mana, washe gari da yammah muna zaune a parlorn Aunty B mukaji buɗe gate da shigowan mota, ba'a wani ɗau lokaci ba yayah Ahmad ya ƙirani a waya yace nazo sama na same shi, ɗaukan ɗan ƙaramin gyalen abayan jiki na nayi na fita.
Ina shiga parlorn shi bakina ɗauke da sallama nashiga, Yayah Ahmad da su M.G nagani zaune a parlorn gaban su cike da kayan snacks da drinks da Aunty J takawo musu, hannun kujeran da yayah Ahmad ke zaune naje na zauna, na ɗaura hannu na a kafaɗan shi na sunkuyo kaɗan setin kunnen shi ina gaishe shi, dariya yayi yana amsa mun, ganin M.G yana kallon mu fuskan shi ɗauke da murmushi, shi kuma A.G ko ɗago kanshi ya kalle ni ma baiyi ba, niko don yau ɗaya na bashi haushi sai na kalli M.G fuskana cike da fara'a nace yayah M.G mun same ku lpy? Shima cike da fara'a ya amsa mun da munzo lafiya? Bayan mun gaisa na juya kan yayah Ahmad ina ce mishi gani.
"Dama M.G ne yace a ƙiraki ku gaisa, shine daman ƙiran, yyh hafsy fa babu wani damuwa ko?" ya faɗa yana riƙe da hannu na da yake kafaɗan shi, murmushi M.G yayi yana kallon mu cike da sha'awa yace, "barrister kuna burgeni kai da ƴan gidanku, kuna ƙaunar junan ku sosai, har sai naji dama ina da ƙani ko ƙanwa mana, da na nuna mata ƙauna kwatankwacin irin naku, amma insha Allahu zan so mata na irin haka da ƴaƴa na", da sauri na ɗago kai na kalle shi, shi kuma ya wani ɗaga mu giran shi duka biyu yana murmushi, sai kawai na samu kaina da maida mishi murmushin.
Baby sis baki gaida A.G ba shine fah ya taso ni akan muzu mu muku sannu da hanya, tun jiya ya matsa muzu naƙi" ya ƙarasa faɗa yana ƙunshe dariyan fuskan shi, "amma wallahi kayi girman banza tunda baka daina ƙarya da ƙazafi ba, munzo dai duba amaryah da ango ba yaran nan marasa kunya ba, bana son jan raini M.G", A.G ya faɗa muryan shi a ɗan cike da ɓacin rai yana hararan M.G, shikuma babu abinda yakeyi sai dariya, yayah Ahmad na tayashi, ni kuma jin abunda A.G ya faɗa sai na maida kallona kanshi fuskana ɗauke da jin haushin yarfen daya mun, harara ya zabga mun, nima ban wani ɓata lokaci ba na zabga mishi harara na murguɗa baki ina guna-guni ƙasa -ƙasa don yaji haushi, ae kuwa nan take ya ƙule, miƙewa yayi da sauri ya tsaya yana duban M.G yace, "tou ƙaton banza maƙaryaci sai ka tashi mu tafi tunda ba'a abun arziki da kai, yanzu sai kaja yarah su raina mutum", ya ƙarasa faɗa yana zungurin ƙafan M.G.
"wani raini kuma? Daga faɗan gaskiya? Tou shikenan muje kada na sake suɓutan baki", ya faɗa yana miƙewa, hannu ya miƙawa Yayah Ahmad yana dariya shima yayah Ahmad ɗin dariyan yakeyi, hararan su A.G yayi ya juya kaina yana kallo na fuska a murtaƙe, kaman baxai ce komai ba sai kuma yace, "ke baki iya suturce jikinki ba ko?" Ban samu daman bashi amsa ba ya wuce ya fita da sauri, nidai kallon kaina kawai nayi naga shigana baiyi muni ba sannan na maida kaina kan su M.G da yayah, suma kallona suke fuskan su cike da dariya, M.G ne yace "kada ki damu baby sis, yau ɗan'uwa na acike da zafin kanshi yake, tunda aka taso da maganan tafiyan mu karatu hankalin shi baya jikin shi, sai faɗa kawai yakeyi," dariya suka sake kwashewa shida yayah, "ae kasan A.G baya wani son tafiyan nan, shi damuwan shi yayi aure, kuma wai ae nigeria ma ana karatu, shi wajen ne baya son zuwa", yayah yafaɗa yana ƙara dariyan fuskan shi, M.G ma dariyan mugunta kawai yakeyi yace, "ae barrister duk inda ya biyo ya rushe maganan tafiyan nan yayi amma Daddyn shi yaƙi sauraron shi, ƙarshe ma ya ɓuge da wai asthman shi yana yawan tashi idan ya fita waje, nan ma Daddyn yace sai yaje dai, haka babu yadda ya iya ya dawo yace shi tou sai yayi aure tukun ya tafi, Daddy ya tmby shi waye yake nema aje ayi magana nan kuma yayi shiru yana muzurai," dariya suka kwashe da shi suna tafawa, M.G ya kalle ni yace, "baby sis ku shiryah gobe in the evening zamu ɗan zagaya da ku kusha iska" godiya na mishi na juya na fita, ina sauƙowa na samu su fatima na gaya musu gobe idan Allah ya kaimu su M.G zasu fita damu shan iska.
******
Wuraren ƙarfe 5:00pm yayah Ahmad ya ƙiramu a waya mu fito, saboda mun saka fita a zuciyan mu tun muna idar da sallan la'asaar muka shiryah, dukkan mu shigan abayah mukayi, Hafsy onion colour, fatima ash, ni kuma blue black nasaka, ko wanmu tayi kyau masha Allah, motan yayah Ahmad shi da Aunty jeeddah ne da Aunty B sai Areefh da yake riƙe a hannunta, sao motan yayah mohd kuma dama yau ya tafi lagos zaiyi 2dys ya dawo, yayah umar da yayah ishaq sai hafsy ne a ciki, motan M.G kuma A.G nagaba sai ni da Fatima abaya, a tsaye a gaban motan muka samu M.G, tou anan muka gaishe shi fuskan shi cike da fara'an shi, yana ta zolayan mu wai munyi kyau kaman zamuje fadan shugaban ƙasa, mudai murmushi dukkan mu mukayi, muna shiga motan wani fitinannen ƙamshi ne yake tashi mai daɗin gaske, fatima ce tafara gaishe da A.G, juyowa yayi kaɗan gefen da take, wato bayan sit ɗin driver ya amsa mata mata, nima a hankali na gaishe shi, amma sai yayi kaman bai jini ba, murguɗa baki nayi na masa gwalo ta bayan shi, don nasan yaji tsaf gaisuwan danayi, narasa dalilin daya sa mutumin nan yake jin haushi na, kome na mishi ohoo, mintsini na fatima tayi a cinya tana harara na, kallon tanayi ina tura baki gaba alaman naji zafin mintsinin, alama ta mun da na gaishe shi, hararanta nayi na sake murguɗa baki a ƙeyan shi na ɗaga kafaɗa alaman naƙi, a haka M.G ya shigo, "*JABI SHOPRITE* zamuje kun taɓa zuwa wurin Aysha"? Ya faɗa yana tayar da motan bayan ya ɗan juyo ya kalle ni, murmushi nayi nace mishi, "ehh muna zuwa, yayah mohd yana kai mu ko yayah Ahmad idan munzo hutu", juyowa kaɗan yayi ya sake kallo na yace, "ok kuna zuwa wa Abbah hutu ne? Na ɗauka su ummie ne kawai suke zuwa", "muna zuwa yawanci a ramadan ko idan mun samu dogon hutu", na bashi amsa, kafin yace wani abu A.G yace, "don Allah malam ka maida hankali a toƙin da kakeyi kada ka chika mun kunne da yawan magana",
Murmushi A.G yayi ya maida hankalin shi kan driving da yakeyi bai tanka mishi ba, a zuciyana nace ganshi kaman wani Boss, na ɗan murguɗa baki na cike da jin haushin shi.
Muna gama yin parking kowa ya fito aka jera ciki, bamu shiga wurin shopping ɗin ba muka wuce wurin shan iska, muna isa muka zauna nida fatima da M.G, ina kallon A.G suka zauna suna magana da Yayah Ahmad, gefe ɗaya kuma yayah ishaq ne da hafsy, Aunties kuma suna tare, bamu daɗe da zama ba M.G ya yafito yaya umar, yana zuwa yace "ga amanan fatima ka tayata hira, bari muyi gefe zan yi magana da Ayshaa please", ya faɗa yana miƙewa tsaye, kallon fatima yayi yace "please teemah a bani aron baby sis zamuyi wani shawara ne da ita," murmushi tayi ta ɗan kalli yayah umar da yake zama tace, "babu komai Allah yasa muji shawara mai kyau", murmushi yayi ya wuce ina biye da shi a baya,
Ɗan gefe dasu kaɗan muka zauna, muna zama na ɗago kaina na dubi inda su A.G suke zaune, abun mamaki sai naga ya bimu da kallo, ɗago kan danayi na kallesu yasa shi harara na, nima ban ɓata lokaci ba na murguɗa mishi baki, dariya yaso bani ganin zaro ido da yayi yana ɗaga mun duka giran shi biyu, alaman na raina shi ko, juyar da kaina nayi kan M.G shiru yayi yana kallo na, kaman baxai ce komai ba, chan sai naji ya sauƙe ajiyan zuciya mai ƙarfen gaske wanda har sai da na ɗago kaina na dube shi.
"shawara zamuyi ni dake baby sis, amma kafin nan ina son ki san waye M.G" kallon shi nakeyi bance komai ba, amma dai na maida hankali na gaba ɗaya kanshi, don na daɗe da wannan burin a zuciyata.
*MUKTAR GARBA (M.G)*
*AUNTY NICE*
managarciya