HAƊIN ALLAH: Labarin Soyayya Mai Rikitarwa, Fita Ta 34 

HAƊIN ALLAH: Labarin Soyayya Mai Rikitarwa, Fita Ta 34 
HAƊIN ALLAH
 
   Labari da rubutawa
       
   *Hauwa'u Salisu(Haupa)
 
 
 
 
 
           Page 34
 
 
Rayuwa kenan, komai na shi ya ƙare, bai da ko sisi bai da abin sisin, shi kaɗai ke rayuwa cike da ƙunci da takura mai taɓa zuciya.
 
Ya rasa abin da yasa har gobe yake jin tamkar ya yi babbar asara ta wani jigo na rayuwarsa, amma ya kasa gane wace asara ce ya yi.  Sau tari ji yake tamkar ya zauna ya bi didduƙin rayuwarsa ko zai gane inda ya rasa wani gurbi amma ya kasa zaman da zai gane ina damuwarsa take.
 
Shi da kanshi mamaki yake idan ya ji hawaye na zubowa daga idonsa, kamar shi wai yana kuka kan yanayin rayuwa! Tabbas abin yana da matuƙar mamaki da ɗaure kai kamar shi ace yana kuka da rana tsaka ba wani laifin da wani ya yi mai ko da wasa. To wa ma ya damu da shi da rayuwarsa a wannan lokacin?
 
 
Ina ne yake da matsala ne wai? Ina ne yake neman ciko a rayuwarsa? Sam bai cikin farin ciki a rayuwarsa. Jin damuwa yake sosai a ransa, ji yake yafi kowa damuwa a wannan rayuwar.
 
Hawaye suka zubo mai masu zafi da ciwon gaske bai damu ba daya goge kawai so yake ya ji fili a cikin zuciyarsa amma abin ya ci tura.
 
Wahala yake sha ta ko'ina ba sauƙi, wuta yake amsa tamkar wanda ke gidan Yari da hukunci mai tsauri haka yake jinsa.
Dama haka rayuwa take wai ga wanda yake cikin damuwa? Dama haka mutum ke jin tsananin tashin hankali da damuwa waɗanda babu musabbabinsu sai dai ka wayi gari ka jika a cikinsu kawai baka san ya zakai ka fita ba kuma.
 
Kamar ba shi ne Deenin nan ba mai nuna isa da taƙama ba. Kamar na shi ne wanda kullum sai ya saka Jiddah a cikin damuwa ba, Yau ga shi a damuwar da tafi wadda yake saka ta.
 
Amma duk da haka bai taɓa jin damuwa ba kan abin da ya yi mata, kawai ɗauka yake wani yanayi ya same shi na rashin kuɗi wanda zai kauce, yana kaucewa kuma zai koma Deenin da wanda ke yadda yaga dama, mai neman duk yarinyar da ya so, mai shiga gidansa cike da izza da gadara, mai juya matarsa yadda ya so, mai nuna mata isa da iko, tai yadda yake so ko da bata so.
Duk sanda ya yi wannan tunanin sai ya ji damuwar ta ɗan ragu, ya ji tamkar komai zai dawo mai yadda yake so yake tsarawa kuma.
 
 
              BAYAN KWANA BIYU
 
 
 
Duk abin duniya ya ishe shi, ji yake tamkar ya ɗora hannu akai ya kwarma ihu.
Yaushe ne wai ya shiga cikin wannan rubibin rayuwar bai ankara ba? Yaushe ne ya faɗa mummunan yanayin nan wai? Gaskiya akwai sake, bai taɓa tunanin akwai irin wannan ranar ba a rayuwarsa. "Jiddah! Ya ambaci sunan cike da jan numfashi mai ɗauke da damuwar gaske. Tun da ya saki Jiddah yake jin tamkar ya rabu da ƙaya ba kamar da ya haɗa mata da gayyar yaranta, sai yake jin damar walawarsa ce ta zo, sai yake jin tamkar shi ɗin dama wauta da kasada ce suka tunzura shi har ya auri Jiddah ya saki jiki har ya haihu da ita. Sai dai kuma ko bayan rabuwarsu sai ya fahimci cewar Jiddah na matuƙar taimaka masa wajen sutura, abinci, kuɗin kashewa, saboda bayan rabuwarsu ne da shekara mahaifiyarsa ta rasu, sai ya sake gane cewa duniya budurwar Wawa ce, domin sai wani munafikin talauci ya addabe shi ya kanainaye shi ya hanashi rawar gaban hantsi.
 
Lokaci guda duk ƴan matan da yake taƙama dasu suka guje shi, domin bai da abin basu, ita kanta Safiya wata uku kenan idan lissafi bai ƙwace ma shi ba da mijinta ya iske su tare cikin ɗakinta suna abin da suka saba, ya tara mai mutane sukai tai masu tofin alatsine ya saki Safiya a gaban jama'a ya kira Mamanta ya gaya mata abin da ya faru, nan take ita ma tace ba dai gidanta ba Safiya hakan yasa ta shirya kayanta tai tafiyarta bai san inda take ba yanzu.
 
Aure yake so amma ya faskara gare shi, duk inda ya je neman aure ba a ba shi, kai tsaye ake gaya mai ba mai iya ba shi yarinyarsa don bai riƙon aure.
 
Sosai abin duniya ke damunsa yadda bai ɓoyuwa daga idanun mutane,duk wanda ya ganshi tabbas yasan yana amsar wuta a rayuwarsa.
 
"Jiddah kaɗai ce zata iya zama da Ni, tábbas mutane sun faɗi gaskiya ke kaɗaice za ki iya jure rayuwa da Ni Jiddah kina ina ne?" Hawaye suka zubo mai "Ban taɓa tunanin za ki iya samun matsayin da zan tuna da ke ba, bayan na rabu dake ba Jiddah. Yau na yarda da cewa duk abin da ya baka tsoro wata rana shi ne zai baka tausayi, domin hakan yake faruwa a tsakanina da ke Jiddah. Tabbas Ni ne abin tausayi a wannan karon yayin da kece abar tsoron."
 
Maƙwabcinsa ya iske shi zaune ƙofar gidan duk ya gwaguye daman kowa yasan cewa Jiddah ita ke gyara gidan idan ya samu matsala, ita ce ke komai na gidan, tun barinta gidan ya fice hayyacinsa kamar yadda maigidan shima ya fita hayyacinsa.
 
Cike da zolaya ya dubi Deeni ya ce, "Malam Deeni ya garin ne naga ka zauna a nan kayi tagumi kamar mai damuwa, na shiga gida na fito na sake iske ka a nan zaune a yanayin dai, ko dai bikin ya matso ne don naji kamar ana maganar aurenka ya matso ko?"
 
Cike da takaici Deeni ya dubi maƙwabcinsa ya ce, "Ai wannan karon ma auren ba zai samu ba, an sake samun munafukai sun shiga sun fita sun raba auren."
 
Cike da nuna alhini ya ce, "Ashsha! Ashsha! Magana ba tai daɗi ba kau, to me zai hana ka maido matarka mai haƙuri da sanin ya kamata ne Deeni?"
 
Wani irin takaici ya ziyarci zuciyarsa ji yake tamkar ya maido baya yanzu, tabbas da babu abin da zai sa ya saki Jiddah ko da kuwa ita ce ta nemi sakin daga gare shi.
 
Ganin ya yi shiru ba mamaki yana hasko wautar da ya yi ne a baya yasa maƙwabcin ya wuce yana ƙara yabon halayen tsohuwar matarsa Jiddah.
 
"Na shiga uku ni Deeni! Ya zan yi ne wai? Ina kike Jiddah? Tabbas zan maida ki ɗakin mijinki ko da hakan na nufin ke baki aminta ba, nasan tabbas waɗanda suka ban ke da farko a wannan karon ma za su sake ban ke Jiddah." Sai yanzu murmushi ya ƙwace mai, har ya samu ƙwarin gwiwar tashi ya koma cikin gidan ya sauya kaya ya nufi gidan Kakannin Jiddah.
 
Ko da ya isa gidan kamar yadda ya zata ba kowa sai Kakarta dake zaune tana saƙar hannu, ya gaidata ta amsa kamar bata so, ya sadda kan shi ƙasa ya ce, "Dama na zo ne in gaya maku cewar na maida aurena da Jiddah, zan sake biyan sadaki ta koma ɗakinta ta cigaba da kulawa da yaranta."
 
Kaka ta dube shi sheƙeƙe ta watsar ta taɓe bakinta ta cigaba da abin da take yi, dukkan alama bata da lokacinsa.
Ya sake maimaita mata abin da ya ce da farko, sai a lokacin ta kalle shi cike da takaici tace, "Amma kai baka da hankali ko? Gidan uban wa naga wata Jiddah balle ka gaya min wai zaka maida aurenka? To daman can Ni nace ka sake ta ne? To tun wuri ka tashi ka ban waje domin Jiddar da ka sani ba ita bace yanzu. Wannan ta girma tasan ciwon kanta ko Ni shakkar yi mata wani abin nake yanzu balle kai da ko  takalmanta bata ba umarnin taka ka ba. Don Allah maza ka tashi kaban waje ai duk naji abin da kai mata da tana gidanka, don haka ban da ta cewa Ni kan aurenka da ita, tana ma Kano bata garin nan sai ka bita can ka gaya mata zaka maida ta ɗakinta."
 
Daram! Gabansa ya faɗi, bai za ci zai samu damuwa da tsohuwar ba, saboda lokacin da ya zo da maganar auren Jiddah tana ta saka albarka tana cewa ko iyayenta na wajen uwa basu yadda ba ita ta amince don haka aure ba zai fasu ba. Amma ji yanzu yadda tai mirsisi ta nuna bata ma san shi ba, wai bata ma iya lanƙwasa Jiddah take nuna mai! Jiddah da ya sani da gudun faɗa da taka-tsan-tsan da abin da zai ja mata matsala da mutum ce take nufin yanzu bata juyowa? Yarinyar da bata da ra'ayin kanta sai wanda aka bata umarnin bi? Tabbas zai jira ta dawo ya tunkare ta kan shi ya gaya mata ya maida ta ɗakinta yasan ba zata mu sa maganarsa ba, tunda daman can bata iya yi masa ko da musu ne balle ya ce mata umarni ne da gudu take aikatawa.
 
Kaka ta sake dubansa fuska ba walwala tace, "Kai Ni don Allah maza ka tashi ka ban waje na gaji da ganinka ma, sai harɗewa nake a saƙar na kasa daidaita zarena."
 
Jiki sanyi ƙalau ya tashi ya fito, amma zuciyarsa na gaya ma shi ya jira Jiddah kawai, ita ce kawai wadda zai sake ma maganar maida aurenta ba wasu ba.
 
Don haka sai ya aje maganar gefe yana jiran dawowar Jiddah daga Kano kamar yadda ya ji ance tana Kanon.
 
Sai dai duk lokacin da yake zaune ko tsaye ko yana tafiya sai kawai idonsa ya dinga hasko mai rayuwar Jiddah a gidansa. Ya dinga hasko yadda take kallonsa idonta cike da hawaye idan ta iske shi da wata a gidan. Ya rasa yadda zai ya daina hasko fuskarta cikin damuwa ko hawaye.
 
Wasa-wasa Deeni ya tsinci kansa cikin wata irin zazzafar ƙaunar Jiddah mai zafin gaske. Duk sanda ya zauna ya hasko ta tana kuka shi ma sai ya kama kukan yana jin kansa a mugu azzalumi wanda ya so kansa fiye da tunanin kowa.
 
A yanzu ji yake Jiddah ita ce kawai jin daɗin rayuwarsa, ita ce kawai wadda ke iya rufa masa asiri a rayuwar nan. Amma tana ina ? Yaushe zata dawo? Shin Hajjo zata amince ya maida Jiddah ma? Bai jin mahaifiyar Jiddah domin mace ce mai sanyin hali mai kauda kai da haƙuri da sanin yakamata ba shakka a gunta Jiddah ta kwaso kyawawan halayenta.
 
Ganin an buge wata guda ba Jiddah ba labarinta yasa Deeni fara cuku-cukun haɗa kuɗin motar da za su kai shi Kano gun Jiddah. A yanzu ji yake idan bai ganta ba a lokacin nan ba tabbas ciwon zuciya zai iya kama shi.
Hakan yasa ya dage da neman kuɗi ta hanyar yin aikin wahala irinsu gini da sauransu don kawai ya tara kuɗin ya tafi Kano gun Jiddah. Ganin tamkar ba zai iya tara kuɗin ba a gunsa yasa ya shiga adashe gun wata Hajiya nan bayan gidansa, duk sati yake zuba Naira dubu uku, da ƙyar yake samun kuɗin da yake kaiwa a sati wani lokacin ma sai ya ƙi ci ya ƙi sha ya haɗa kuɗin da ƙyar ya kai mata, burinsa shi ne ya haɗa kuɗin mota dana sadakin da zai bata shike nan ya wuce gun.
 
Sai da ranar kwasa ta zo tun da safe ya shirya tsab ya ɗauki ƴan kayansa ya isa gidan Hajiya mai adashe, ya zabga sallama yana ta washe baki don ji yake tamkar an biya mai Makka tunda zai ga Jiddah Yau a gabansa. Ko da yake bai san unguwar da take ba, amma daga nan yana amsar kuɗin gidan mahaifiyarta zai je ya amshi adireshin gidan Hajjo ya wuce yasan ba zata hana shi ba.
Sai da ya yi sallama sau uku sannan Hajiyar adashen ta fito fuska ba yabo ba fassala ta dube shi tace, "Yauwa har ka iso ashe? Daman jiranka nake ai ka zo."
 
Fuska kamar gonar auduga haka Deeni ya washe baki yana ta murmushi tsabar farin ciki ma ya kasa ko da amsa mata tambayarta.
Ta wage baki ta ƙwalawa yarinyarta Hanifa kira, sai kuwa ga wata budurwa ta fito daga cikin gidan.
Hajiyar adashe ta dubi Deeni ta fito da kuɗi Naira dubu talatin ta ƙirga cif tana kallonsa tace, "Kaga kuɗi nan Naira dubu talatin ko?" Deeni ya ɗaga kanshi yana murmushi tace, "To ba naka bane, nawa ne, domin sune adadin kuɗin da na kashe wajen zubar mata da cikin shegen daka ɗirka mata a shekarun baya." Ta saka kuɗin cikin jakarta ta shige gida yarinyar na zabga mai harara domin bata manta tsinannen dukan da akai ta mata ba jeri-jeri sanadin cikin da ya yi mata ba a gidansu.
 
Jagwab! Deeni ya zauna ba shiri zufa ta wanke mai jiki nan take ya ji wani irin zazzaɓi ya rufe shi don haka ya ja jiki ya kama hanyar gidansa idonsa na zubar hawaye. Wai me yasa yanzu komai ke kwance mai ne? Me yasa baki ɗaya lissafinsa ke kwancewa ne ba sadda ya so ba? Har ya isa gidansa hawaye ke kwaranya idonsa tamkar an buɗe fanfo.
 
Nan da nan hadari ya taso aka fara ruwa tamkar da bakin ƙwarya, ya yi nisa a tunanin abin da ba zai ce ga shi ba ya ji wata irin ƙara har ya zabura ashe bangon gidansa ne suka zube baki ɗaya sai ɗakin kawai a tsaye tsakar gidan, daga inda yake yana hango hatta toilet ɗin ya afka lokaci guda da katangun.
 
Komawa ya yi ya zauna ya kasa ko da furta kalma guda ko raya kalma guda a ransa. Jinsa yake tamkar ba mutum ba, ji yake yafi kowa matsala a duniyar, ji yake yafi kowa damuwa a duniyar.
Yanzu ya zai yi kenan? Waye gare shi da zai taimaka mai ya gyara gidansa? Ta ina zai samu ganin Jiddah yanzu? Sai a lokacin hawaye suka zubo mai tuna Jiddah da ya yi, lokacin da take gidan bai damuwa da duk abin da ke samun gidan domin ita ce ke shiga ta fita ta gyara, hatta wutar gidan ita ce ta jawo ta, take biyan kuɗin wutar duk lokacin da ake biya bai san ma nawa ake biya ba shi sam. Abu guda ya sani idan aka yanke wutar bata biya ba ya dinga mata masifa kenan yana faɗan don me zata bari a yanke wutar. Sai ga shi yanzu tunda ta tafi ba wuta gidan domin bai iya biya, haka ya haƙura ba don bai son hasken ba sai don bai da halin biyan. 
A bayan rabuwarsa da Jiddah ya fahimci cewar ita ce rufin asirinsa ita ce mai biya mai buƙatu bai sani ba yana ta hauka, hatta kayan sawarshi yanzu duk sun tsufa sun lalace babu na kirki dama ita ce idan ta yi sarin kaya Kano take ware mai wasu ta ba shi tun daga takalma yadi shadda hadda ƙananan kaya yanzu duk sun lalace kuma bai da halin siyen wasu. 
Tsananin tashin hankali yasa zazzaɓi ya rufe shi nan inda yake yana ji mutane na sallama don jajanta mai abin da ya faru na zubewar katangun gidansa amma ya kasa amsawa, har suka gaji suja juya ba tare da sun leƙo ba sunga halin da yake ciki ba a cikin ɗakin.
 
Wasa-wasa har dare yana kwance cikin azabar ciwo ga ƙishirwa yana ji ga shi bai iya tashi ya ɗebo ruwa ya sha. Hakan yasa ya tuna lokacin da Jiddah ke kwance cikin ciwo ga uban ciki amma ya kasa yi mata alfarmar ɗebo mata ruwa idan ta roƙa, haka zatai amai ya dinga mata masifa yana faɗa ba tausayi haka zai tada ta ya ce dole sai ta kwashe shi ko mutuwa za tai sai ta kwashe aman bai damu ba. Bai manta akwai ranar da take wani irin ciwon kai tana kwance a falo sai nishi take shi kuma jin haushin nishin yake don haka ya fito ya tsaya a gabanta ya ja tsaki ya ce, "Malama kin dame ni da nishi har kin hanani barci cikin salama ya kike so nayi ne ina jin barci kuma Ni?" Cikin azabar ciwon ta buɗe idonta ta ƙyar tace, "Kai haƙuri, kaina ne kamar zai tsage biyu don ciwo ga zazzaɓin dake damuna." Tsaki ya ja ya fice daga gidan yana masifar ta tabbatar tayi barci kafin ya dawo a ranar.
 
Yau ga shi kwance cikin jinya yana jin ƙishirwa ba mai ba shi ruwa babu mai yi mai sannu shi ma. Duk yadda yake mata idan bata lafiya bata nuna mai komai haka idan ciwo ya kama shi zata siyo mai magani idan ma ya cika kwanciya ta ba shi kuɗi tace ya je asibiti yaga Likita, abin da bai taɓa yi mata ba kenan bata kuɗin magani, to shi da ke ɗauke maganin ma ya saida idan ta siyo ko Mamarta ta sai mata? Hawaye suka cigaba da zubo mai yana jin nadama da takaicin abin da ya faru a baya tsakaninsa da Jiddah. 
 
Sai bayan sallar ishsha'i ya samu da ƙyar ya miƙe ya sha ruwan kuma sai amai, sosai ya dinga aman dan da nan ya galabaita ya kasa ko da kakarin aman, ya kwanta ƙasa yana jan numfashi. Mijin Binta ne ya ganshi kwance da alamar ba lafiya, ya shiga cikin gidan yana kiran sunan Deenin.
 
Kasancewar Deeni daman irin raggwayen nan ne a gun ciwo yasa yake kwance yana ta kuka kamar ƙaramin yaro. Cikin hanzari ya kama shi ya kai shi ɗaki yana mai sannu da jiki ya ƙara da yi mai jajen abin da ya faru na zubewar katangun gidansa.
 
Shi dai ba baka sai kunne sai kuwa kukan da yake wanda har ga Allah ba kukan komai bane illa na nadamar abin da ya yi ma Jiddah.
 
Ji yake yana matuƙar son ganinta, sosai yake son ɗora idonsa kanta. Soyayyarta ke yawo a sassan jikinsa ko da yaushe ita ce a cikin ransa, yana yawan tuna abubuwan da ya yi mata na takurawa da gadara duk ta shanye ta haƙura bata taɓa nuna mai ɓacin ranta ba, sai ranar da ya zage ta ranar ne kawai ta nuna mai ɓacin ranta har ta kwantar da shi jinyar kwanaki.
 
Lallai ya yadda da mutane da suke cewa  Jiddah matar arziƙi ce, tabbas yanzu ya amince domin ita ce arziƙinsa ya fahimta yanzu. Bata da son kai haka bata ɗaukar muguwar shawara akansa komai za a ce mata ya yi bata tankawa haka shima bata taɓa tsare shi ba kamar yadda ya sha ganin matan abokansa na turke su idan suka yi nisan kiwo basu koma gidan ba. 
 
Yana jin yadda abokansa ke yawan ƙorafi kan matansu idan suka haihu suna tada masu hankali kan sai sun yi masu kaza da kaza abin da bai taɓa faruwa ba tsakaninsa da Jiddah. Shi idan ta haihu ma shike cinye duk abin da ta samu kuma bata nuna ko a fuska ta damu.
 
Yaushe zai sake samun mata kamar Jiddah ne? Yaushe zai samu dama irinta baya ne ta sake auren Jiddah?  Tabbas auren Jiddah shi ne kawai abin da zai sa shi a cikin hasken rayuwa a wannan baƙar rayuwar da yake yi amma ta yaya hakan zai faru ne?
 
Mijin Binta ya miƙe tsaye yana cewa, "Deeni ka rage tunani bai da amfani ka ɗauki haƙuri Allah da Ya baka ikon gina gidan nan shi ne zai sake baka wata damar insha Allah." Ya fice yana jin tausan Deenin a ranshi yadda lokaci guda komai ya sauya mai.
 
Cikin ƙarfin hali ya samu ya fice waje yana addu'ar Allah Ya ba shi ikon haɗuwa da wanda zai sai ma shi ko da ruwan shayi ne ya sha domin yunwa yake ji sosai kuma bai da ko sisi.
 
Haka ya dinga gararanba amma bai dace da wanda ya ba shi ko da Naira ɗari ba, har ya yanke tsammani ya nufi hanyar gidansa ya ji an kwaɗa mai kira, yana juyawa ya ga ƙanin Jiddah da suke Uwa ɗaya suka gaisa ya tambaye shi yara don yasan suna gidansu ya ce mai suna lafiya lau, cike da jin nauyi Deeni ya tambaye shi ko zai samu wani abu gunsa bai da lafiya ga yunwa yana ji. Ya yi jim sai kuma ya ce, "Ba damuwa, Yaya  Deeni nima wallahi ban da ko sisi garin ya yi zafi sosai don haka na kira Aunty Jiddah na gaya mata sai ga shi yanzu ta turo min da dubu goma, sune ma na fito na cire. Mu je na fitar sai na baka ai ba wani abu an zama ɗaya." Wata matsiyaciyar kunya ta rufe Deeni, watau Yau ma arziƙin Jiddah zai ci kenan, abin kunya ma ta hanyar ƙaninta. Duniya kenan makaranta.
 
Bayan sun je ya cire kuɗin ya ce su je gun mai shayin ya sai mai shayi mai kauri ya haɗa mai da ƙwai biyu ya biya kuɗin ya kawo Naira dubu ya ba shi ya wuce. Tabbas Jiddah dabance a rayuwarsa basu tare amma ya ci albarkacin ta. Har zuwa yanzu halin Jiddah na kirki na nan kenan na taimako da kyautatawa wanda take tare da shi. "Jiddah ina sonki matata." Hawaye suka biyo bayan furucinsa.
 
Sai da ya yi sati yana ciwon, sannan ya samu sauƙi, sosai yake jinjina abubuwa da dama da suka faru gare shi daga rabuwa da Jiddah kamar ya rabu da samunsa kamar ya rabu da farin cikinsa haka yake ji koma ya ce ke faruwa gare shi.
 
Cikin sati guda da zubewar katangun gidan ya koma kamar wani sabon kamun hauka tsabar tunani da neman ganin Jiddah ido rufe yasa ya koma kamar sabon mahaukaci. Hatta mutane sun ankara da yadda ya koma kamar ba shi ba, duk ya jeme ya lalace ya zama abin tausayi, duk wanda ya zauna da shi sai ya gaya mai irin zaman da ya yi da Jiddah ya ce kuma yanzu haka ya maida ta.
 
 
Ganin abin na neman zamar ma shi hauka yasa danginsa suka tausaya mai suka ba shi kuɗin mota suka ce ya je Kano gun Jiddar ya dawo da ita a ɗaura masu aure. Suka haɗa kuɗaɗe su kai ma gidan danni suka dai gyara mai iyakar ƙarfinsu.
 
Ya shirya tsab ya isa gidansu Mama ya shiga ba kunya ba tsoron Allah ya tambaye ta adireshin gidan da Jiddah take, duk da ba ƙaramin razana ya yi ba da yaransa suka kasa gane shi ba wanda ya kuka shi wasansu kawai suke duk da an gaya masu shi ne mahaifinsu.
 
 
Mama ta gaya mai komai ta bishi da fatan alheri ya fice kai tsaye ya nufi tashar mota ya faɗa motar Kano suka ɗauki hanya.
 
A cikin motar ne wani mutum ke ta bada kabarin wata shari'a mai ɗaure kai da ban mamaki da ake a Kaduna da wata fitacciyar Lauya mai suna Barista Alawiyya Bello Gareji amma ranar Shari'ar bata je kotu ba sai wata sabuwar Lauya mai ɗinbim basira da iya magana ta je a mamadinta wadda ba  shakka an fahimci yadda Alƙalin ke amsar uzurinta alama ce ta kai tsaye yana sonta mai suna Barista Jiddah... Yauwa kunga an sako hotonta ma ao gaskiyar magana ko ni da ina da wasu manyan kuɗaɗe sai na yi Wuf da ita.
 
Kamar shi ake ba labarin haka ya ji musamman daya ji an ambaci mai irin sunan matarsa Jiddah don haka sai ya bi sauran mutane masu kallon wayar shi ma ya kalla yaga Baristar da ake magana kanta.
 
Wata uwar ƙara ya saki ya fisge wayar ya yana ƙare mata kallo kar yadda kallo ya koma kansa.
 
 
Don kun matsa ne na yi wannan ɗin ku dau haƙuri.
 
Taku a kullum Haupha ✍️