Gwamnatin  Kebbi ta ƙaryata labarin  ɓarayin daji sun  karɓe ikon wani ƙauye a Jihar 

Gwamnatin  Kebbi ta ƙaryata labarin  ɓarayin daji sun  karɓe ikon wani ƙauye a Jihar 
Gwamnatin  Kebbi ta ƙaryata labarin  ɓarayin daji sun  karɓe ikon wani ƙauye a Jihar 
 
Daga Sani Twoeffect Yawuri
 
Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi Sanata Umar Abubakar Tafida ne ya ƙaryata wannan labarin da cewar bashi da tushe balle makama.
 
Haka kuma ya bayyana labarin da cewar ƙirƙirar ƙarya ce kawai irin ta masu rubutu a yanar gizo.
 
Mataimakin Gwamnan ya ƙara da cewar Gwamnatin Jihar da haɗin guiwar jami'an tsaron Jihar suna bakin kokarin wajen tabbatar da zaman lafiya a fadin Jihar da kuma bayarda kariya ga dukkanin ƙauyukan Jihar daga dukkanin wani hari na ɓata gari ko ƴan ta'adda.
 
Mataimakin Gwamnan ya bayyana hakan ne ranar talata  a lokacin da yake wata zantawa ta musamman da manema labarai a garin Birnin Kebbi fadar Gwamnatin Jihar.
 
Mataimakin Gwamnan ya tabbatar da labarin da ya faru a garin Mera wanda Yan ta'addan Lakurawa suka kaima hari wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane goma sha bakwai (17) in da suma al'ummar garin Mera suka yiwa 'yan ta'addan raunuka a bata kashin da aka yi a lokacin harin.
 
Bayan samun labarin wannan harin ne Jami'an Gwamnatin Jiha da 'yan Majalisu suka kai ziyara a ƙauyen kuma suka bayar da tallafi daban-daban tare da tabbatar da jami'an tsaro sun ɗauki dukkanin matakan da suka dace na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.