Mutanen Zamfara Sun Kauracewa Zaben Kananan Hukumomi

Mutanen Zamfara Sun Kauracewa Zaben Kananan Hukumomi
 

An gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar Zamfara a yau Asabar 16 ga watan Nuwambar 2024. 

Sai dai al'umma da dama ba su fito zaben ba kamar yadda ake tsammani yayin da suke cigaba da gudanar lamuransu. 
Channels TV ta ce wasu 'yan birnin Gusau da dama sun bubbude shagunansu yayin da ake gudanar da zaben. 
Hukumar zaben jihar (ZASIEC) ita ta shirya zaben a kananan hukumomi 14 da na kansiloli da ke fadin jihar. 
Sai dai mutane ba su fito zaben ba saboda wasu dalilansu na karan kansu wanda ya kashe armashin zaben da aka yi a yau Asabar.
Wasu sun alakanta samun matsala a fitowar al'umma da cewa rashin wayar da kan mutane da hukumar zaben jihar ta yi. 
Wani mai suna Abubakar Abubakar ya ce kwata-kwata bai san ma da zaben ba saboda haka dole ya bude shagonsa domin gudanar da kasuwanci.
Duk da rashin fitowa zaben, hukumar ta gudanar da zaben ba tare da samun matsala musamman a bangaren tsaro ba.