Gwamna Abba ya bayar da Umarnin koyar da sana'o'i ga matasa 'yan Jihar kano
Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bada umarnin fara daukan dalibai da kuma yi musu rajista a Makaratun gaba da sakandare na Koyan Sana’o’i na Musamman guda ashirin da shida (26) wanda ke fadin Jihar Kano.
Wannan Makarantu/Cibiyoyin koyar da sana’o’i an samar dasu neh tun zamanin Mulkin Senata Rabiu Musa Kwankwaso. Sai dai Gwamnatin Ganduje (shekara 8 data shude tayi watsi da wannan Cibiyoyi masu muhimmanci, tare da kulle su, wanda yayi sanadiyyar korar dalibai da kuma lalacewar gine gine a wannan makarantu.
Ganin haka yasa Gwamnan Jihar Kano Alh. Abba Kabir Yusuf ya bada umarnin fara gyara da kuma sabunta wannan Cibiyoyi da zasu taimaki matasan mu wurin dogaro da kai da kuma tabbatar da al’umma mai inganci a fadin Jihar Kano.
Tuni dai aikin sabunta wannan Cobiyoyi yayi nisa, inda an kammala wasu, sauran kuma sun kusa kammaluwa, tare da samar da kayan aiki na zamani.
Dalibai zasu amfana wurin koyan sana’o’i kamar noman zamani, kimiyya da fasaha, harkan tsaro, wasannin zamani, kere-kere da dai sauran su.
Bisa wannan kuduri na Gwamna, daya daga cikin wannan cibiyoyi da aka kammala, wato “Kano Reformatory Institute, Kiru” za ta fara aiki nan take.
managarciya