Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa ya kulle iyakokin ƙasa na ƙasar nan ne, domin ya ƙarfafawa ƴan Najeriya guiwa su riƙa samar da abincin da za su ci.
Shugaba Buhari ya bayyana cewa duk da an soki wannan hukuncin na sa da farko, daga baya 'ƴan Najeriya sun koma suna yabawa, rahoton The Cable ya tabbatar.
Shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a ranar Talata, lokacin da ya ke ƙaddamar da sabuwar hedikwatar hukumar hana fasa ƙwauri ta ƙasa, wacce ta laƙume N19.6bn wajen ginata.
Sabuwar hedikwatar tana a yankin Maitama, cikin babban birnin tarayya Abuja.
Shugaba Buhari ya yi nuni da cewa Allah ne kaɗai zai iya kare iyakokin ƙasar nan saboda tsawon da su ke da su, cewar rahoton The Nation.
"Ina son ku sani cewa daga tafkin Chadi zuwa Benin Republic ya fi tsawon kilomita 1,600, don haka Allah ne kawai zai iya kare iyakokin nan.
Ana buƙatar mutumin da ya cancanta da ƙarfin da zai iya sanya ido a kai."
"Da gangan na kulle iyakokin ƙasar nan saboda na san 'ƴan Najeriya, za su yi odar shinkafa, su kai wata Nijar da sauran ƙasashe, sannan su shigo da shinkafar nan."
"Da arziƙin da mu ke da shi, mu na da mutane, mu na da ƙasa da yanayi mai kyau. Ƙasashe nawa ne su ke da sa'a a duniya kamar Najeriya, ƙasashe ƴan kaɗan ne.
"Don haka kulle wannan iyakar mai tsawon kilomita 1,600, ƴan Najeriya sun haƙiƙance sai sun ci shinkafa ƴar waje. Ko dai ku ci abinda ku ka noma ko ku mutu. Na yi ƙoƙarin bayyana matsayata, sannan daga baya ƴan Najeriya sun yaba da hakan."